• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Jaddada Ƙudirin Ƙarfafa Ƙawance Da Indonesiya

by Sulaiman
1 year ago
Indonesiya

Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin ta na zurfafa alaƙar ta da ƙasar Indonesiya, tare da mai da hankali kan batun tattalin arziki da kuma hanyoyin haɗin gwiwa.

An tabbatar da hakan ne a taron Indonesiya da nahiyar Afrika karo na biyu, wanda ake gudanarwa daga ranakun 1 zuwa 3 na Satumba, 2024, a Bali, babban birnin ƙasar.

  • NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa 855 Kan Kowace Lita 
  • Zanga-zanga: Ana Tuhumar Mutane 10 Da Laifin Cin Amanar Kasa

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa Babban Taron Haɗin Gwiwa na Masu Ruwa da Tsaki da kuma Taron Shugabanni a ƙasar da ke nahiyar Asiya.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

Ministan ya nanata ƙudirin Nijeriya na ƙulla ƙawance da Indonesiya, yana mai cewa dukkan yankunan biyu suna da abubuwa da yawa da za su samu daga ƙara haɗin gwiwa a fannin kasuwanci, zuba jari, da musayar ilmi da ƙwarewa.

Ya ce: “Taron Indonesiya da Afirka wata hanya ce ta haɗin gwiwa, da nufin ciyar da ƙasashen mu biyu zuwa makoma mai haske da wadata.”

Idris ya ƙara da cewa, “Nijeriya ta ƙudiri aniyar yin amfani da ƙarfin da muke da shi da albarkatun mu don mai da hankali kan muhimman ginshiƙai kamar sauyin tattalin arziki, makamashi da haƙar ma’adinai, samar da abinci da lafiya, da tattalin arziki na dijital.

“Waɗannan su ne ginshiƙan da za a gina haɗin gwiwar mu a nan gaba, tare da zurfafa haɗin gwiwa da cigaban tattalin arziki mai ɗorewa wanda zai amfani dukkan al’ummomin mu.”

Taron ya jaddada gagarumin ƙarfin tattalin arziki da al’ummar Afirka da Indonesiya suke da su, waɗanda ke wakiltar sama da mutane biliyan 1.7 da jimillar ƙarfin tattalin arziki na GDP na dalar Amurka tiriliyan 4.4.

Taron ya tattaro shugabannin ƙasashe, jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa, da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, inda suka tattauna haɗin gwiwar tattalin arziki, da magance matsalolin duniya, da kuma lalubo hanyoyin samun cigaba mai ɗorewa tare.

Jagorancin Nijeriya wajen ciyar da ajandar Tarayyar Afirka ta 2063 shi ma ya kasance jigon tattaunawa a taron.

Ministan ya yi bayani kan cikakkiyar ajandar Shugaban Ƙasa Tinubu ta sauye-sauyen tattalin arziki, tsaro, shugabanci, da cigaban al’umma a matakin ƙasa, da kuma ƙoƙarin da yake yi na inganta harkokin kasuwanci a yankin, da ababen more rayuwa, da kwanciyar hankali a siyasance ta hanyar jagorancin sa a Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

An bayyana rawar da Nijeriya ke takawa a Yankin Kasuwanci na Nahiyar Afirka (AfCFTA) a matsayin babbar hanyar bunƙasa kasuwanci da masana’antu a cikin Afirka.

Taron, wanda ya samu halartar wakilai daga ƙasashen Afirka 22 da kuma wasu ƙasashe biyar da ba na Afirka ba, ya kuma tuna da taron nahiyoyin Asiya da Afirka na shekarar 1955, wanda aka fi sani da “Bandung Spirit”, wanda ya aza harsashin dangantakar Asiya da Afirka.

Taron ya yi kira da a ƙara inganta yin mu’amala a tsakanin nahiyoyi ta fuskar kasuwanci, zuba jari, da haɗin gwiwar raya ƙasa.

An jaddada cewa kamata ya yi Afirka ta zarce matakin mai fitar da ɗanyen man fetur kawai, ta zama cibiyar samar da kayayyaki, tare da ba da tabbaci na musamman ga ayyukan bututun iskar gas da ke ratsa sahara tsakanin Nijeriya da Aljeriya da kuma Moroco.

Taron na Indonesiya da Afirka ya kasance wani dandali na ƙarfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Indonesiya da ƙasashen Afirka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Next Post
Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Najeriya

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Najeriya

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.