Babbar tawagar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagles ta gamu da ragowar matsayi a fagen iya taka leda a Duniya kamar yadda alkaluman da hukumar kwallon kafa ta FIFA ta fitar a baya bayan nan wanda ta wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis.
Tawagar da Augustine Eguavoen ke jagoranta ta fadi zuwa matsayi na 44 daga matsayi na 36 da ta ke a baya,kuma sun koma matsayi na biyar a iya taka leda a Afirika daga matsayi na hudu da suke a kwanakin baya.
- Hukumar FIFA Ta Dage Gasar Cin Kofin Afirka AFCON Zuwa Shekarar 2026
- Tattalin Arziki: Gwamna Lawal Ya Nemi Hadin Gwiwar Masu Zuba Jari Na Kasashen Afirka A Taron AFREXIM A Kenya
Ana hasashen faduwar ba zata rasa nasaba da yadda kungiyar ta nuna rashin katabus a wasanninta na karshe na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta 2025,inda kasar dake yammacin Afirka ta tashi kunnen doki 1-1 da Jamhuriyar Benin a Cote d’Ivoire, sannan suka sha kashi a hannun Rwanda da ci 1-2 a Uyo.
Kasar Morocco ta ci gaba da zama ta daya a Afirka, inda Senegal da Aljeriya da Masar ke matsayi na biyu da na uku da na hudu,a ranar 14 ga watan Disamba ne za a fitar da jadawalin FIFA na shekarar 2024 na karshe,amma kuma babu wani fatan da Nijeriya ke da shi na hawa sama saboda babu wata wasa da zasu buga kafin wannan lokacin.
Kasashen Argentina da Faransa da kuma Spain ne suka ci gaba da zama a matsayi na daya zuwa na uku, inda Ingila da Brazil suka cigaba da zama a cikin kasashe biyar na farko.