Khalid Idris Doya" />

Nijeriya Ta Samu Koma-Baya A Mizanin Yaki Da Rashawa Na Duniya

Kasar Nijeriya ta samu koma-baya a mizanin yaki da cin hanci da rashawa na duniya a shekara ta 2019.

Nijeriya ta yi kasa da matsayi biyu baya a jerin kundin shekara-shekara da ake bugawa kan tace lamuran rashawa.

A rahoton kididdiga na shekara ta 2018, Nijeriya ta kasance ta dari da arba’in da hudu (144) a jerin kasashe da jama’ar su ke da laifukan rashawa da cin hanci, kamar yadda hukumar duniya mai bin ba’asi kan wadannan munanan lamura ta zayyana. Nijeriya yanzu ita ce ta dari da arba’i da shida (146) bisa wannan ta’asa, a cikin kasashen duniya dari da tamanin (180) kamar yadda rahoton ya nuna.

Nijeriya ta cimma kashi ashirin da bakwai (27) ne cikin kashi dari a shekara ta 2018 karkashin CPI, kamar yadda ta cimma a shekara ta 2017 na CPI, don haka kokarin ya fado kashi na arba’in da uku (43).

Exit mobile version