Nijeriya ce kan gaba wajen fannin kiwon dabbobi a Afirika ta yamma, musamman ganin cewa, yadda ma fi yawan ‘yan kasar suka fi mayar da hankali a kan kiwo, a yankin Arewacin kasar kuma suna yin noma.
Ministan noma da raya karkara Dakta Mohammad Abubakar ne ya bayyana hakan a wajen taro da aka shiry akan, shirin kawo sauyi kan kiwo na kasa da aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja.
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Ra’ayin Yakin Cacar Baka Da Manufar Kama Karya
- Manufar Sin Ta Fadada Bude Kofa Ga Waje Za Ta Tallafawa Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya
Dakta Mohammad ya ce, mata da matasa fiye da kashi 30 cikin dari ne suka rungumi shirin kiwata dabbobi, domin su dogaro da kansu ta hanyar samun kudi da abinci.
A cewar Dakta Mohammad, adadin yawan amfanin da ake samu da kuma yadda ake amfani da shi a Nijeriya ya bambanta sosai ,inda ya yi ninu da cewa, fannin kiwo ya kasance wani muhimmin bangaren tattalin arzikin kasa da kuma kara samar wa manoman kasar nan riba.
Ministan ya ce hakan ya taka rawar gani a fannin tattalin arzikin kasa baki daya, inda ya sanar da cewa, ya kai kusan kasha biyu zuwa biyar na kasa da kasha goma na tattalin arzikin kasar.
Ya kuma bayyana cewa, kididdigar da aka yi a baya, bayan nan ta nuna cewa, an wadata fannin kiwon dabbobi da shanu kimanin miliyan 264 da awaki miliyan 88 2 da tumaki miliyan 503 da alade miliyan 8 9.
“Kiwo ya kasance wani muhimmin bangaren tattalin arzikin kasa da kuma kara samarwa da manoman kasar riba”.
“Hakan ya taka rawar gani a fannin tattalin arzikin kasa baki daya, inda ya sanar da cewa, ya kai kusan kashi biyu zuwa biyarna kasa da kashi goma na tattalin arzikin kasar.
Dakta Mohammadya ci gaba da cewa, a fannin kiwon kaji ana da miliyan 465, agwagi miliyan 36 4 talo-talo miliyan 38 sai zomaye miliyan 55 sai rakuma 353 173 da jakuna 1 234 284”.
A cewarsa, a bisa kokarin ma’aikatar a shekara ta 2021 ya sa al’ummar ta zama kan gaba wajen noma da kiwo a yammacin Afirika.
Ya ce ma’aikatar tana kara fadada tare da zurfafa hadin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki da cibiyoyi da suka dace don magance matsalolin da fannin kiwon kasar nan ke fuskanta.
Ma’aikatarsa da hukumar aikin noma ta kasa ne suka shirya taron a babban birnin tarayyar Abuja, mai taken taron mayar da masana antar kiwon dabbobi ta Nijeriya don a bunkasa tattalin arzikin a karni na 21.
“Ma’aikatar tana kara fadada tare da zurfafa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki da cibiyoyi da suka dace don magance matsalolin da fannin kiwon ke fuskanta”.
A cewar Dakta Mohammad, taron ya zo a kan gaba idan aka dubi yadda Nijeriya takarkatar da hankalinta wajen yunkurin kara habaka tattalin arzikinta ta hanyar noma.