Tsokacin yau zai yi duba ne dangane da irin gudunmawar da mata ke ba wa ‘yan uwansu Mata a lokutan shagulgula ko makamancin haka, wanda ake kiransa da biki.
A bisa al’adar malam bahaushe, a duk lokacin da aka tashi yin wani shagali kamar; Suna, Bikin Aure, taron kara shekara, Saukar karatu, ko abin jajantawa kamar: Dubiya, Rasuwa da dai sauransu, a kan ware wasu kudade ko wasu abubuwa na musamman wanda za a bawa uwar taro ko Amarya, a matsayin gudunmawa.
- Wa Ya Dace Al’umma Su Zaba?
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Ra’ayin Yakin Cacar Baka Da Manufar Kama Karya
Yayin da ita kuma wadda aka bawa za ta yi godiya a lokacin. A duk lokacin da taron wadda ta ba da gudunmawa ya tashi ita ma haka za a hada mata goma ta arziki me sunan gudunmawa, a takaice dai Mata na taimakon junansu da gudunmawa.
Sai dai a yanzu wannan al’amari ya canja salo tare da kara ta’azara ta yadda wasu suka maida shi tamkar bankin da ake masa zubi zuwa lokacin kwasa, domin kuwa mafi yawa a yanzu ga duk wadda ta bayar da gudunmawa na jiran lokacin da za a rama mata bikin, madadin a kai mata kasa da wanda ta bayar ko kuma daidaida wanda ta bayar, sai a mayar mata da fiye da abin da ta bayar.
Wasu mutanen na kin zuwa guraren tarukan da aka gayyace su sabida rashin halin gudunmawar daza su bayar.
Gudunmawar a yanzu ba ta tsaya iya manya magidanta, iyaye ba, har ma da kanana masu tasowa (Matasa), ta yadda wasu ke kukan irin wannan matsala da ke hana su tara kudaden da za su yi wa kansu abun arziki, wanda hakan ke sa wa wasu Matan na samun gidajen share-share da wanke-wanke dan samun kudaden da za su bayar na gudunmawa, wanda wasu ke kiran hakan da Biki.
Ba komai ya sa su hakan ba face cin burin tara musu mafi yawan abin da suka bayar kafin aurensu, ko makamancin haka, al’amarin dai a yanzu ya zama tamkar zuba jari.
Sai dai shi wannan biki a duk lokacin da wanda aka yi wa bai samu damar ramawa ba, ko da kuwa ba shi da shi, hakan yakan zaman masa abun fada wajen jama’a, wasu ma har su bi bashi tunda sun riga da sun yi musu tun a baya, idan kuwa ba a yi ba ya zama dan zani, ya zama abin gori, ya zama abun ka ce na ce a bakunan mutane, a takaice kenan.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Ko me ya sa ake yin hakan?, Ko su ma Maza suna yin hakan?, Mene ne amfani ko rashin amfanin yin hakan?, Me hakan ke haifarwa? Inda suka fayyace nasu ra’ayoyin kamar haka:
Aisha Musa Yankara daga Jihar Kano:
Wannan abun ya zama kamar dan lada ake sallah kenan, wannan abun ba dole bane amma kuma an kusan zamar da shi dolen, saboda idan wance za ta yu biki idan baka bata wani abu ba, kai ma idan naka ya tashi ba za ta baka ba, sai dai a baka na jin kunya amma mafi akasari ba za a baka ba, da an yi magana a ce ai nima da bikina ya tashi ba ta yi mun ba. Toh kin ga kenan abun ya kusan zama kamar dole toh kuma daman dan lada ake sallah gaskiya ko ni yanzu na ba da dubu aka maido min 500 wallahi Allah ban kara bayarwa, sabida dan lada ake sallah, taimakekeniya ne fa. Toh ni dai a tunanina kamar Maza sun fiyin hadaka (Kungiya) a hausance Ajo, duk da matan ma suna yi a ce a hada kaza kaza in wane zai yi hidima a hada a bayar, gaskiya mafi yawanci Maza sun fi yin haka, amma kuma su kamar na kar kara yawanci za ki gani abinci ne za a yi abinci wannan ya yi abinci a kai gidan wane, wannan ma in zai yi hidima akai gidan wane, kin ga shi wannan kawai ba za a ce su ma Maza suna yi ba, amma ban san wani yankin ba. Eh! toh! Amfanin yin hakan, taimakekeniya ne, saboda wannan ‘yar gudunmawar da za a baka maganar Allah fatana taimakawa shi kuma rashin amfaninsa kai! gaskiya ba shi da wani rashin amfani. Hakan yana haifar da abubuwa da yawa, maganar Allah me ba ka kullum baka da kamar shi kake gani, ina daya daga ciki ina yi, ai duk duniyar ma a haka take tafiya kaso 90 a cikin100% suna yi.
Fadila Lamiɗo daga Jihar Kaduna:
Tabbas! Irin wannan bikin ya zama ruwan dare, ki ba da gudunmawa idan sha’aninki ya tashi a baki mafi yin shi, sai dai a nawa tunanin hakan ba daidai ba ne, domin bai zama abun sha’awa ba sam!, hakan ya zama dora wa kai wani nauyi ne wanda a karshe zai iya zama takura a gareka, saboda ko ya tsunmu ba daidai suke ba, abun da ya fi da cewa a tunanina shi ne; idan sha’anin waninka ya taso ka samu abun da Allah ya hore maka ka ba da, kuma kar ka ba da shi da zummar wai za a maido maka dole, abun nufi ka yi domin Allah kawai, gudunwa tana taimakawa sosai ga wadda ya ki cikin sha’ani, shi yasa ma aka kira shi da gudunmawa, kenan ana nun fin agazawa, dan haka gudunmawa bai kamata ya zama biki ba, idan kana da shi kana iya yin sama da abun da aka baka tunda da ma agazawa ce, idan baka da shi kuma ka ba da kasa da shi, idan ma babu gaba daya kar ka takura kanka, domin idan ya zama da takura, ranar biya kana cikin tashin hankali toh sai mu canza mu shi suna daga gudunmawa ya koma bashi da ruwa, ni dai ina daga cikin masu ba da gudunmawa ba biki ba, kuma shawara ta ga wanda suka mai da shi biki da su canza shi ya zama gudunmawa ko in ce tallafawa hakan ne zai sa abun ya zama abun sha’awa.
Aisha Sani Abdullahi (Zayishatul-humairath) Jos Marubuciyar Hausa:
Wannan dabi’a ce da al’umma suka dasa cikin rayuwarsu karfi da yaji, tabbas! ihsani/ kyauta suna da dadi matukar gaske, amma na kokarin mai da hakan tamkar ibada wanda sam! bai da ce ba, ra’ayi ne ga masu halin ba da wasu bada kawai, amman ba wa iya zama dole ba. Tabbas! Maza ma sun fara tasowa da wannan dabi’ar dalilin matansu, za ki ga namiji ya ce “lokacin da matata ta haihu ai ni matarsa ba ta kawo mun komai ba don haka ni ma ba zan bada ba”, ko ya ce ai “lokacin bikina ni ma bai ban komai ba don haka a nashi nima dan kallo ne. Da amfani wajen kyautawa da taimakon juna, rashin amfaninsa kuwa ya dangana ne ga yadda ake kokarin maida wa dole ga mai karfi da mara karfi. Yana haifar da rabuwar kan ‘yan uwa ko abokai. A Shawarce shi ne; wanda ya yi niya kuma yake da karfin badawa kawai ya ba da ba tare da tunanin maido masa makamanci ko ninkin hakan ba.
Hassan Hamisu Rijiyar Tsamiya Daura:
To gaskiyar magana wannan tsari da Hausawa ke yi na gudunmawa na biki ko suna, abu ne mai alfanu domin bahaushe mutum ne da aka san sa da taimakon dan uwansa da hadin kai. Sai dai abin da za a lura da shi anan shi ne; a halin yanzu Hausawa sun canza yanayin da iyayenmu suka yi a baya, in da a halin yanzu idan mutum bai mayar da abin da aka yi masa a bikinsa ba sai ya zama abin surutu a dangi. Gaskiya maza ba su da irin wannan tsarin domin su suna tallafawa junansu ne ba domin batun a dawo masu da abinda suka bayar ba. Gaskiya wannan tsari yana da amfani na tallawa tsakanin al’umma. Sai dai inda rashin amfaninsa yake tsawwalawa kai abin da wasu ba za su iya bada kuma rashin yi wa juna uzuri. Bana daga cikin masu yin wannan bikin, Shawarata a gare su kawai shi ne; duk abin da za su yi su yi don Allah.
Muhammad Sabi’u (Nauyi) Jihar Kano Nijeriya:
Wata sabuwa kenan in ji ‘yan caca, wannan batu gaskiya abu ne muhimmi ga duk kan wani bahaushe nagari, domin kyakkyawar al’adata ce da magabatanmu ke yi sai dai fatan da muke kawai duk abin da za mu yi mu yi don Allah. Su Maza za a iya samu masu yin hakan amma gaskiya sai a karkara domin a nan ne za ka ga abokai sun gina wa abokinsu gida ko daki ba tare daya na nan ba, amma a birni gaskiya maza ba su yi. Gaskiya ni ban ga wani rashin amfani a cikin aikata hakan ba. Ba na cikin masu yin hakan gaskiya sai dai kungiya da muke da ita ta shabbabul-khairi da mukan tara kudade domin taimakawa abokinmu da zai yi aure da abincin da za a bawa jama’a da ruwan sha. Shawarata ga masu aikata hakan su ci gaba domin abu ne mai kyau matuka, kuma komai za su yi wa dan Adam su yi don Allah.
Khadeeja Muhammad (Kanty kankanaty) daga Kasar Saudia:
Gaskiya ba dole ba saboda wasu ne suke haka na ce kamar hausawa suna haka sun dauke shi kamar dole in ka kawo wa mutum wani abin wai dole rana na ta ita na yi mata irin haka gaskiya bai kamata wannan abun, kamar ba shi kenan, in ba haka ka yi wa mutum kyauta, sannan kana tunani shi ma zai maka, a gaskiya wannan abun bai kamata suna yi ba, dan haka dan Allah a daina irin rashin hankalin nan. Gaskiya maza ba su yin wannan rashin hankalin an bar wa mata. Gaskiya ba shi da amfanin amma bada gudumawa da juna yana kara mutanci da junansu. Babu abin da zai haifar sai rashin zaman lafiya ga juna. Ni dai gaskiya shawarata shi ne; dan Allah a daina irin wannan abun gaskiya bai kamata ba, sannan in za su yi wa junansu su yi saboda Allah ba dai ba shi ba.