Idris Aliyu Daudawa" />

Nijeriya Za Ta Dauki Nauyin Babban Taro A Kan Cutar ‘Lassa fever’

Cibiyar hana yaduwar cututtuka da kuma maganin su ta kasa ta shirya tsaf saboda yin taro na farko wanda kuma na kasa da kasa ne, ba a kuma taba yin irin shi ba, saboda a tattauna dangane da cutar zazzabin Lassa a kasar Nijeriya.
Shi dai taron za ayi shine tsakanin ranakun 16 da kuma 17 na watan Janairu, taken taron shine ‘Shekaru Hamsin na cutar zazzabin Lassa yadda za a dauki matakin hana yaduwarta’. Taron zai yi bikin shekarau hamsin da gano kwayar cutar zazzabin Lassa a Nijeriya.
Wadanda ake sa ran zasu zo wurin taron su ne kwararru a bangaren kiwon lafiya, masu bincike, da kuma masana ilimin kimiyyya,. daga sassa daban -daban na duniya, wadanda suka dace suna yion ayyuka, akan shi zazzabin Lassa, bama kamar tun lokacin da cutar ta bulla.
Lokacin taron masu bincike daga kasashe wadanda suke dawani al’amarin ita cutar Lassa, suma za su iya musayar ra’ayi, da kuma bayar da shawarwarin yadda za a shawo kan matsalar ita cutar.
Babban jami’i kuma shugabar ita hukumar Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka lokacin da ya kira taron ‘yan jarida, kafin a kaiga yin shi taron, wanda yanzu Nijeriya ce take daukar shugabanci na kokarin da ake yi na yadda za ayi maganin ita cutar gaba daya, ya zama ta daina yaduwa ko kuma ya kasance babu ita ko kadan.
“ Zamu yi taron kimiyya ne saboda mu samu yin musayar ra’ayi akan, dalilin da ya sa za muyi aiki tare, saboda samun cikakken hadin kai.
“ Muna yin bikin shekarun 50 tun lokacin da aka fara gano ita cutar zazzabin, saboda mu tursasa ma kan mu, mu yi abubuwa masu yawa. Mun yarda ko kuma amince da za muyi aiki tare, saboda a samu rashin mutuwa a sanadiyar shi zazzabin na Lassa. Wannan muna sa ran zai sauka kasa da kashi 26, a yanzu dai abin muna son na da shekaru biyar abin ya kasance bai kai kashi 10 ban kamar dai yadda ya kara jaddadawa”.
Mista Ihekweazu ya ci gaba da bayanin cewar shi taron wannan ya nuna ke nan Nijeriya ta nuna cewar da gaske take yi, na al’amarin daya shafi cutar zazzabin na Lassa, saboda rayuwar mutanen da ita Hukumar take son cetowa.
Ya ci gaba d bayanin za ma atattauna dangane da ita allurar rigakafin wato irin halin da ake ciki akan su alluran da ake son ayi saboda maganin cutar.
“ Mun yi abubuwa da yawa amma kuma mun san cewar da akwai bukatar mu kara yin wasu, a lokacin taron zamu rika yin musayar ra’ayi, mu kuma rika sauraren sababbin shawarwari, mu kuma samu sababbin abokai, daga nan kuma sai kuma a fara wasu yarjejeniyoyi wadanda suke nasaba da kimiyya.”
Ya ci gaba da bayanin cewar shi taron zai taimmaka ma Nijeriya,, bayan haka kuma wasu masana akan al’amarin kiwon lafiya, a wurin taron, a bada bayani abin da aka sani dangane da ita cutar, ilimin da ake da shi, sai kuma abubuwanda suka kamata ayi wadanda suka hada da muhimmancin yin bincike akan ita cutar.
Wasu kasashe na yammacin Afirka sun taba samun annobar cutar zazzabin Lassa.
Nijeriya ta saba haduwa da barkewar annobar zazzabin a ko wanne sashe na kasa, jihohi kamar Edo, Ondo da kuma Ebonyi, koda wanne lokaci sune wadanda suke kasancewa a jago jihohi wadanda suke fuskantar annobar.
Sai dai kuma wani abu mai daure kai shine jihar Borno wurin da aka gano ita cutar tun farko, akwai lokutan da bata samun wani aukuwar barkewar ita annobar.
A shekarar 2018 Nijeriya ta bayar da babbar aukuwar ita annobar, tun lokacin da tarihin shi zazzabin ya fara, inda jihohi 21 suka bayar da rahoton barkewar ita annobar, a kalla wanda ake sa ran ya kamu da cutar.
Da yake bayani akan muhimmancin yin shi taron Elsie Ilori wanda shi shugaba ne nakwamitin kwararru akan cutar Lassa, ya bayyana cewar, karuwara yadda ake kamuwa da ita cutar, ya sa an yi wau tambayoyi, wannan kuma shi yasa, muka fara yin tunani, sosai da sosai, akan wurtaren da suka kamata ayi bincike, saboda mu kara maida hankali saboda maganin ita cutar ta zazzabin na Lassa.”
“ Tun daga wancan lokacin ne muka fara al’amarin bincike na cutar Lassa ta kasa, da kuma wani abinda muka yi saboda mu gano su kwayoyin cutar, daga nan kuma sai mu kara bangaren sa idon mu,. yadda za a shawo kan cutar, ga kuma al’amarin tuntuba ta sadarwa, da kuma sauran abubuwan da suka kamata ayi.
Misis Ilori ta bayyana cewar Nijeriya ta hadau da barkewar annobar cutar da yawa, yawancin su, suna kasancewa ba agano su ba, saboda al’amuran yadda ita kasar take.
“ Cikin kwanaki biyun da za a yi muna sa ran zamu hada kai da sauran al’ummar duniya, saboda ayi duk yadda ya dace ayi, wajen nuna shedun abubuwan da suka faru, wadanda kuma su zamu yi amfani dasu wajen kare lafiyar al’ummar Nijeriya kamar yadda ya kamata. Bugu da kari kluma muna sa ido saboda mu ga yadda shi kokarain namu zai sa su abokan huldar namu, su hada kai da mu wajen sani wasu abubuwa danagane da ita cutar zazzabin Lassa, a wannan lokacin da aka kokarin kawo karshen ta.
Shima da yake bada tashi gudunmawar wadda kuma duk kamar yadda wanda ya fara jawabin ya yi, Emmanuel Agogo wanda shine shugaba na kwamitin kwamitoci na kimiyya, ya bayyana cewar bayan an kammala da al’amarin da ci gaban da ake yi na abubuwan da suke za a iya samun bayan su ta yanar gizo, da kluma wadanda ba za’ a iya ba. Akwai dai takardu fiye da 350 wadanda aka gabatar, daga ciki kum,a an zabi 160.
“ A cikin kwanaki masu zuwa muna sa ran sauraren kokarin da aka yi, sai kuma kokarin da aka yi wanda ya zarce dukkan wadanda aka yi a baya, saboda shi zazzabin cutar Lassa. Muna kira da masana ilimin kimiyya wadanda muke dasu gida Nijeriya, su sa ran ganin sakamakon shi taron da za ayi. Hakakanan kuma muna kira da ‘yan Nijeriya su yi ma bakinmu barka da zuwa, wadanda suka zo daga kusa da kuama nesa, wannan taro na farko na kasa da kasa akan zazzabin cutar Lassa.”
Ya bayyana cewar shi taron yana da wasu wuarar tara wadanda suma suna da bukatar a duba su.
1. Yadda za a sa ido da kuma maida hankali akan yadda cutar take da kuma yadda take yaduwa
2. Yadda za a fuskanci ita cutar idan har ta kai ga barkewaCase management of Lassa and other BHFs
3. Yadda za ayi gwaji saboda gano ita cutar
4. Yadda za a bada bayanai ko labarai danagane da ita cutar
5. Yadda al’umma za su taimaka wajen kokarin da ake yi
6. Yadda cutar take da kuma maganin ta
7. Kula da lafiyar dabbobi da kuma muhallin su, saboda al’amarin yana da alaka da su
8. Tsare- tsare da mmaniufofi da kuma yadda za a aiwatar dasu duk dai saboda ayi maganin ita cutar
9. Alluran rigakafi da kuma bullo da wasu abubuwan da zasu taimaka

Exit mobile version