Assalamu alaikum, jaridar LEADERSHIP A YAU Juma’a, gaisuwa cikin farin tare da fatan alheri nake ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga ‘yan’uwa da abokan arziki kamar su Hassan Mai Nasara Babayo, tare da Sulaiman Yusuf mai kanfanin S.Y Ingawa (LTD), sai kuma Umar Sani Madaki, tare da Musa Yusuf Ingawa wato Acid Quality Designer, da kuma Ibrahim Muhammad inkiya Zola, da Alshak Muhammad, sai Ibrahim Tukura inkiya Shugaban Matasa, tare da Usman Hamisu, sai Adam Ibrahim Dan Barno, da kuma Malam Falalu Abdullahi wanda hake Zaria City, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Abba Abdullahi inkiya baka son tsufa. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin sunna amin. Barka da Juma’a.
Daga Muhammad Idris (Babanne), Abuja.
07065279510
Salam, ina farin ciki tare da godiya ga wannan fili na Goron Juma’a, ina so a mika gaisuwar Goron Juma’a ga yarana Zainaf Ahmad, tare da Adam Ahmad, sai kuma Sadik Ahmad, da Halima Ahmad, sai Yusuf Ahmad, da Maimuna Ahmad, tare da Siyama Ahmad, sai Uwar Gida sarautar Mata Madam Suwaiba, da kuma Nasiru wanda ya tafi Saudiyya da iyalansa, tare da Sa’idu Gulu a karamar hukumar Rimin Gado a garin Kano, sai kuma Alhaji Nura a karamar hukumar Kabo, da Isa Reza a garin Masanawa Kabo, da kuma Yakubu Garo, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Majidadin Kofa Bala Ibrahim. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin.
Daga Ahmad Namalan Kano.
08034041022
Gaisuwa cike da farin ciki nake mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Yusuf Isa, sai kuma Mahmud Bashir, tare da Faisal Sani, da Hauwa Isa, sai Rashida Isa, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Maimuna Isa. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Iliyasu Isa, Abuja.
08169130801
Dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a da masoyana kamar su mai gidana Farfesa Musa Yakubu, sai kuma ‘ya’yansa Raji Musa Yakubu da Aminu Musa Yakubu, tare da Fatima Hamisu, da Imam Ahmad, daga korshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Mustapha Hamisu. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Usman Hamisu, Kaduna.
08160874213
Da farko, ina mika sakon Goron Juma’a ga abokaina Muhammad Danladi, sai kuma Muhammad Idris mai shago a Lake View Homes Phase 2, Abuja, da Mahmud Abubakar, tare da Abubakar Isa Manaja, da kuma Yahya Haruna, da Surajo Aliyu, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Bello Inuwa. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Alhaji Ibrahim Isa, Bida City.
08065123244
Dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga makusantana kamar su Alhaji Murnir Wanbai, sai kuma Alhaji Sulaiman Garki, tare da Malam Abdullahi mai sayar da katin waya a Garki, da Alkali Badarawa Kaduna, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Tijjanin Alhaji Nura dake Garki Abuja. Dafatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Malam Zilkibilu Garki, Abuja.
07034661195
Assalamu aikum. LEADERSHIP A Yau Juma’a, ina farin cikin da samar mana da dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya kara wa wannan Jaridan tamu farin jinni da daukaka a fadin Duniya baki daya. Da farko, ina mika gaisuwar Goron Juma’a ga manyan abokanaina Malam Bala wanda ya ke garin Zaria inkiya dan kasa nagari, sai kuma Raheenah Masaka da Ikleemacy, tare da Anti Hanane, da kuma Masoyiyata wato Fatima da Muhammad Idris, daga karshe ina mika gaisuwar Goron Juma’a ga Mahaifaya ta A’sha Baffa. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, ami summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Aliyu Muhammad, Bauchi.
07060664230
………………………………………………………………………………………………………………………
Muhawarar Masu Karatu Ta Makon Jiya
A makon jiya mun kawo muhawara kamar haka:
Tsakanin Hannu da kuma Baki wanne ne ya fi aikatuwa a jikin Dan’adam?.
Hannu Ya Fi Aikatuwa
Assalamu alaikun LEADERSHIP A YAU Juma’a, gaskiya a ganina hannu ya fi aikatuwa a jikin Dan’adam. Dalili kuwa shi ne, kamin ma a sami abin da bawa bakin sai hannu ya sarrafashi. Haka kuma za ka iya wuni kana yin aiki kowani iri da hannu, amma ana wuni ba a ci ba.
Daga Imrana Jabi, Abuja.
0907573726284
Baki Ya Fi Aikatuwa
Assalamu alaikum LEADERSHIP A YAU Juma’a, gaisuwa ga ma’aikatan LEADERSHIP A YAU, tabbas hannu yana bayar da gudummuwa sosai ga jikin Dan’adam, amma gaskiyar magana baki ya fi aikatuwa duba yadda baki ke bayar da gudummuwa wajen gina gangan jikin Dan’adam tun daga ranar da mutum ya zo duniya har zuwa ranar da zai mutu. Da furucin baki ake gani dai-dai, sannan taa baki Dan’adam ke cin abinci.
Daga Yahaya Mai Kaza Kajiji, Legas.
08080323435
Baki Ya Fi Aikatuwa
Assalamu alaikun LEADERSHIP A YAU Juma’a, gaisuwa mai yawa ga ma’aikatan LEADERSHIP A YAU, nawa ra’ayin dai shi ne, baki ya fi hannu aikatuwa. Saboda za ka iya yin magana sau dari, amma ba ka motsa hannuwanka ba.
Daga Yahaya. M. G. Liman Kabauri Kiru, Kano.
081544754149
Gaisuwa da jinjina ga dukkan ku da kuka fadi irin na ku ra’ayi. Hakika kun yi rawar gani muna godiya.
………………………………………………………………………………………………………………..
Sabuwar Muhawara
Wai tsakanin dangin miji da dangin amarya, su wa suka fi kashe kudi wajen bikin aure?
Za ku iya aiko mana da ra’ayinku ta wannan lambar 08034980391 ko ta email dinmu: leadershipayaujumaa@gmail.com sai mun ji daga gare ku.