Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), reshen Jihar Ribas, CIS James Sunday, ya kai ziyarar aiki ga Mai Girma Gwamnan Jihar Ribas Sir Siminalayi Fubara, a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal.
James ya bayyana cewa ziyarar ta fi mayar da hankali ce kan hadin gwiwa da ci gaba a fannin zuba jari, tsaron cikin gida da sauran fannonin ci gaba. Yayin da ya yaba da irin karimci da girmamawa da gwamnan ya nuna wajen karbar bakuncin tawagarsu duk da dimbin ayyukan da ke gabansa.
Kwanturola James Sunday, ya yi amfani da wannan damar wajen mika godiya a madadin mukaddahiyar shugabar hukumar, kan hidima da goyon bayan da gwamnatin jihar ke bai wa hukumar ta NIS tare da tabbatar wa Gwamna Siminalayi Fubara kudirin hukumar na kara sadaukar da kai domin aiki tare da sabuwar gwamnati domin ci gaba, da tsaron kasa da kuma al’ummar jihar Ribas baki daya.
Kwanturolan ya nanata doguwar alakar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar da Hukumar NIS, tun a shekarar 1967, lokacin da aka kirkiro Jihar Ribas daga yankin Gabashin Kudu a ranar 27 ga Mayu, 1967, kuma daga baya aka kirkiro Jihar Bayelsa daga tsohuwar Jihar ta Ribas a ranar 1 ga Oktoba, 1996, inda kirkiro da Karamar Hukumar Omuma a rana guda da tsame Bayelsa, ya kara yawan kananan hukumomin jihar zuwa 23.
Hukumar Shige da Fice tana da manyan jami’ai da ke kula da yanki a kananan hukumomi 23 da hedikwatarta da ke Fatakwal babban birnin jihar da kuma ofishin fasfo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp