Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta ƙaddamar da sabon ingantaccen fasfo da ake wa laƙabi da “enhanced e-passport” tare da buɗe ofishin da zai riƙa samarwa a Ottawa da ke yankin Ontario a ƙasar Kanada, domin bai wa ‘Yan Nijeriya mazauna ƙasar damar samun sabon fasfon mai matakai daban-daban.
Nijeriya dai tana daga cikin ƙasashe biyar na duniya kuma ta farko a Afirka da suka samar da sabon ingantaccen fasfon. Shi dai sabon fasfon, an tsara shi ne da fasahohin zamani tare da inganta tsaro a cikinsa da kuma ƙara yawan samfuransa ciki har da mai shafi 64 da ke aiki har na tsawon shekara 10 domin ƙara kyautata walwalar ‘Yan Nijeriya masu balaguro a ƙasashen duniya.
Sakamakon tsaron da aka ƙara a sabon fasfon ta fuskoki 25 fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu, maɓarnata da masu satar shaida ba za su iya amfani da shi ba wajen damfara.
Da yake jawabi a yayin ƙaddamarwar, Kwanturola Janar na NIS, CGI Isah Jere Idris, ya bayyana cewa duk da fara bayar da sabon ingantaccen fasfon a Kanada, za a ci gaba da bayar da tsohon da sabon a tare har zuwa lokacin da za a kammala aikin fasfunan da aka nema a baya.
“Za a ci gaba da bayar da sabon ingantaccen fasfon da kuma wanda ake bayarwa kafin zuwan sabon har sai lokacin da aka mayar da ɗaukacin cibiyoyin bayar da fasfo zuwa na sabon da aka samar”, ya bayyana.
Har ila yau, CGI Isah Jere ya ce za a magance tsaikon da ake samu wajen yi wa mutane fasfo matuƙar masu nema suna bin matakai da ƙa’idojin da aka shimfiɗa ta hanyar tabbatar da cewa sun gabatar da buƙatarsu ta fasfo ta shafin intanet tare da biyan kuɗi ta nan, da daidaita bayanan fasfonsu su yi daidai da bayanan da ke ƙunshe a katinsu na shaidar ɗan ƙasa (NIN).
Isah Jere ya ƙara jaddada cewa NIS za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta sauke nauyin da tsarin mulkin ƙasa ya ɗora mata tare da kyautata mu’amala da abokan hulɗa a ko ina cikin faɗin duniya.
A nashi jawabin tun da farko, Ministan Cikin Gida, Rauf Ogbeni Aregbesola, ya bayyana cewa sakamakon ƙaddamar da ofishin sabon fasfon a Kanada, a halin yanzu ‘Yan Nijeriya mazauna can za su iya shiga shafin NIS na intanet su gabatar da buƙatunsu na fasfo kai-tsaye.
Ya ce, wa’adin da aka ɗiba ga mai neman sabon fasfo shi ne za a yi masa a cikin mako shida, yayin da wanda zai sabunta kuma za a yi masa a cikin mako uku. Waɗannan makonnin da aka ɗiba a cewar ministan, domin a bai wa NIS sarari ne ta yi bincike game da bayanan da mai neman fasfo ya gabatar da kuma tabbatar da ingancin aikin kamar yadda ake yi a duk ƙasashen duniya da suka ci gaba.
Haka nan ya nanata muhimmancin daidaita bayanan fasfo da na katin ɗan ƙasa (NIN), domin a cewarsa, ana matuƙar samun matsala kan haka kuma da zarar an samu bambanci komai ƙanƙanta, za a samu tsaiko wajen aikin fasfon.
Wakazalika, da yake tofa albarkacin bakinsa, Jakadan Nijeriya a Kanada, Mista Adeyinka Asekun ya yaba wa Ministan da Kwanturola Janar na NIS bisa hoɓɓasar da suka yi wajen ƙaddamar da sabin ingantaccen fasfon a Kanada wanda ya ce ita ce ta uku da NIS ta samar da sabon fasfon baya ga Amurka da Ingila.
Ya shawarci ‘Yan Nijeriya da ke ƙasar su yi ƙoƙari su ci gajiyar wannan damar da NIS ta samar musu musamman wajen neman fasfo mai shafi 64 da ke aiki na tsawon shekara 10 wanda ake iya neman sabuntawa tun ana saura shekara ɗaya wa’adin aikinsa ya ƙare.