Babban Kwanturola na hukumar shigi da fici ta kasa (CGI), Muhammad Babandede (MFR), ya bayyana tsarin da hukumar na shi ta yi na yanda za ta yi aikin sa ido da kuma [akinta da ta tanadar na musamman domin lura da sha’anin tsaro a kan yanda zabe ke gudana, a shalkwatar hukumar da ke Abuja, a matsayin wani sashe na irin gudummawar da hukumar za ta bayar na ganin an gudanar da babban zabe na 2019 lami lafiya da kuma kara karfafa tsarin Dimokuradiyya na kasar nan.
Da yake magana a wajen bikin kaddamarwan, babban Kwanturolan ya yi nuni da cewa, shi wannan dakin na kula da yanayin da zaben ke tafiya, zai yi aiki ne a duk tsawon yini da dare ba hutu, a kwanakin zaben, zai kasance a bude ne domin karban rahotanni da koke-koke a kan komai da ya shafi zaben, a duk sassan kasar nan.
Babban Kwanturolan Babandede, ya nanata shawarar da ya baiwa wadanda ba ‘yan kasan nan ba na kar su kuskura su tsalma bakin su a kan yanda zaben ke gudana.
ASanarwar da jamiín yada labaran hukumar, DCI Sunday James ya rattaba wa hannu, ta ce shugaban hukumar ya kuma bukaci al’umman kasar nan da suke da duk wani labari mai ma’ana na wasu da ba mutanan kasar nan ba da suke sa hannu a kan sha’anin zaben, ko kuma suke da wani koke da ya shafi hukumar ta shigi da fici a kan yanda zaben ke gudana, da su hanzarta tuntuban sashen sa ido a kan yanda zaben ke gudana, ko kuma su kira dakin da aka bude na musamman domin kula da yanda zaben ke gudana kai tsaye, ko su hanzarta kiran kowace daya daga cikin wadannan lambobin wayan.
Lambobin sun hada da: 08053789496, 08093363797, 08067989523 and 09028007451