Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice na Jihar Ribas, James Sunday, ya yaba wa jami’an da suka jajirce wajen gudanar da ayyukansu karakshin shirin ‘Operation Shigan Bultu.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Kwanturolan ya fitar a ranar Alhamis.
- INEC Ta Ayya 29 Ga Maris A Matsayin Ranar Zaben Cike Gurbi A Adamawa
- Magoya Bayan PDP Sun Yi Zanga-Zanga Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kaduna
Kwanturolan wanda tsohon jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ne, ya ce rundunar za ta sanya ido kan ma’aikatan da ke nuna rashin da’a ko duk wani ma’aikaci ya yi watsi da matsayin aikinsa ko kuma ya gaza yin abin da ake tsammani.
Ya gargadi jami’an hukumar kan wasa da aikin da ke samar musu da albashin da suke dauka duk wata.
Ya ce “Dole ne mu bai wa aikin da babban Kwanturola-Janar ya ba mu, sabon aikin zai sa ido kan ayyukan manyan ma’aikat ciki har da ni kaina.”
Ya bukaci abokan aikinsa da su ja hankalinsa a duk lokacin da ya kaucewa hanya, wanda a cewarsa aiki ne na hadin guiwa.
Kana, ya ce babu wanda za a yarda ya yi kasa a guiwa wajen gudanar da aikinsa, inda ya ce dole ne kowa ya zage damtse a duk lokacin da yake bakin aiki.