NIS Ta Dakatar Da Yin Sabon Fasfo Har Sai…

Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede

Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa ta dakatar da karɓar buƙatun masu neman yin sabon fasfo ko sabuntawa daga ranar Talata 18 ga Mayun 2021 har sai zuwa 31 ga watan domin ta samu damar biyan bashin da ya taru mata na fasfon.
Shugaban hukumar CGI Muhammad Babandede ya bayyana haka a ranar Talata a wani taron manema labaru da ya gabatar a shalkwatar hukumar da ke Sauka, a kan hanyar filin jiragen sama na Abuja.
Babandede ya ce sun yanke shawarar ɗaukar wannan matakin ne bisa umarnin Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola. Wanda ya buƙaci a kammala sallamar waɗanda suka riga suka gabatar da buƙatar fasfon a baya kafin a ci gaba da yin sabbi da sabuntawa waɗanda nasu ya kammala aiki.
“A bisa ƙoƙarin da muke yi na kyautata yanayin ayyukanmu na fasfo da kuma bai wa kowane ɗan Nijeriya haƙƙinsa na ɗan ƙasa, mun dakatar da karɓar buƙatar yin sabbin fasfo ko sabuntawa daga yau (Talata) 18 ga Mayun 2021 zuwa 31 ga watan.”
“Za mu yi amfani da lokacin wurin duƙufa ga aikin biyan bashin fasfon da ba mu yi ba. A halin yanzu muna da isassun takardun fasfo a ƙasa da za su isa mu sallami duk wanda ya riga ya gabatar da buƙatarsa. Mun kulle dukkan hanyoyin biyan kuɗin fasfon sai mun kammala da wanda muke da shi a ƙasa.” In ji shi
Babandede ya bayyana cewa kar wani ya yi tunanin zai bi ta ɓarauniyar hanya wajen neman yin fasfon a tsakanin lokacin da aka dakatar, domin a cewarsa sun ɗauki ƙwararan matakai na daƙile hakan da kuma yaƙar masu karɓar cin hanci da rashawa. Ya ce sun naɗa jami’ai na musamman da za su sanya ido wajen tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin da suka shimfiɗa, yana mai gargaɗin cewa duk wani jami’i da aka kama da ƙumbiya-ƙumbiya ya yi kuka da kansa.
Har ila yau, ya bayyana cewa, daga ranar 1 ga watan Yuni za a ci gaba da karɓar buƙatun masu neman yin sabon fasfo da masu sabuntawa, inda za su yi cikakken aiwatar da tsarin bayar da fasfon cikin mako 6. Haka nan ya ce a halin yanzu hukumar ta bayar da dama ga ‘Yan Nijeriya cewa za su iya sabunta fasfonsu tun ana sauran wata 6 wanda yake hannunsu ya gama aiki, inda ya ce wannan dama ce ga kowa ya sabunta fasfonsa cikin kwanciyar hankali ba sai lokaci ya ƙure ba mutum ya zo yana mazurai yana nema cikin gaggawa.
Wakazalika, CGI Babandede ya yi kira ga duk waɗanda suke neman fasfo da kar kowa ya tafi ofishin fasfo har sai an ba shi damar ya je, inda ya ce an yi tsari na aika wa kowa saƙon wayar hannu na lokacin da zai je. Don haka babu ɗan bora ko ɗan mowa, kowa za a yi masa aiki bisa gaskiya da adalci.
Ya kuma yi gargaɗi a kan a guji bayar da cin hanci ga jami’ai da sunan samun fasfo cikin hanzari, inda ya ce akwai layin waya da suka bayar a shafinsu na intanet domin kai rahoton duk wani jami’i da ya nemi cin hanci a bakin aiki. Ya ba da tabbacin cewa da zarar sun samu ƙorafi za su yi bincike a kai kuma tabbas za su hukunta duk wanda aka kama da laifi.
A bisa bayanan da CGI Babandede ya nuna wa manema labaru ta hoton majigi, ana bin hukumar bashin fasfo a cikin gida wajen dubu saba’in da ɗaya da ɗari shida da arba’in (71,644), inda a ƙasashen waje kuma ake bin ta dubu goma shabakwai da ɗari da tara da shida, kuma ya ba da tabbacin cewa za su kammala cikin yardar Mai Duka a tsakanin lokacin da suka ɗiba.
Zuwa yanzu dai NIS ta bayar da fasfo ga ‘Yan Nijeriya kusan sau miliyan 15.
Exit mobile version