Abdulrazaq Yahuza Jere">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

NIS Ta Kafa Karin Sabbin Manyan Ofisoshi Hudu Domin Karfafa Kula Da Iyakokin Kasa

by Abdulrazaq Yahuza Jere
March 26, 2021
in LABARAI
1 min read
NIS Ta Yaye Mataimakan Kwanturola Janar Da Suka Halarci Kwas Na 10

Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede ya tabbatar da kafa sabbin manyan ofisoshi na musamman guda hudu domin karfafa kula da iyakokin kasa.

Sabbin manyan ofisoshin sun hada da wanda za a kafa a Idi-Iroko da ke Jihar Ogun, da na Mfum da za a kafa a Kuros Riba, da na Jibiya da ke Jihar Katsina sai kuma na Illela da ke Jihar Sakkwato.

Shugaban na NIS Babandede ya tabbatar da kafa sabbin manyan ofisoshin ne domin cika umarnin da Ministan Cikin Gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayar na mayar da kashi 50 bisa dari na yawan jami’an hukumar zuwa sassan da ke kula da iyakokin kasa.

Sakamakon daga darajar ofisoshin, an tura manyan jami’ai masu mukaman Kwanturola domin su shugabance su, inda za su rika kai rahoton aiki ga manyan jami’ai masu mukaman Kananan Mataimakan Kwanturola Janar da ke kula da manyan ofisoshi na shiyya.

Sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NIS, DCI Sunday ya fitar, ta yi karin hasken cewa wadannan sabbin manyan ofisoshin kari ne a kan wanda ake da shi a iyakar kasa ta Seme domin bai wa hukumar dama kara kaimin sanya ido ga mutanen da ke shige da ficen kasa domin kula da iyakoki kamar yadda ya kamata da kuma inganta tsaron kasa.

 

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugabannin Sin Da Kamaru Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diflomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Next Post

Wani Rahoto Da Ya Kunshi Karairayi Da Yawa

RelatedPosts

Malamai

Kungiyar Malamai Ta Tallafa Wa ‘Yan Hijira Sun Shirya Taron Bita Na Ramadan

by Abdulrazaq Yahuza Jere
1 hour ago
0

Daga Mustapha Ibrahim, Kungiyar Hada Kan zauran Malamai da kungiyar...

Zakzaky

Ramadan: El-Zakzaky Ya Raba Tallafin Abinci Ga Mabukata

by Abdulrazaq Yahuza Jere
1 hour ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad, Shugaban harkar musulunci a Nijeriya (IMN)...

Musulmi

Wajibi Ne Musulmi Su Ajiye Bambancin Akida Dan Hadin Kai Da Samun Zaman Lafiya – Shareef Ishak  

by Abdulrazaq Yahuza Jere
1 hour ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, An bayyana cewar wajibi ne musulmi...

Next Post
Wani Rahoto Da Ya Kunshi Karairayi Da Yawa

Wani Rahoto Da Ya Kunshi Karairayi Da Yawa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version