• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NIS Za Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Bayar Da Sabon Ingantaccen Fasfo A Zariya Da Daura

...Yayin Da Ganduje Ya Kaddamar Da Katafariyar Cibiyar Wallafa Fasfo A Kano

by Sabo Ahmad
3 years ago
NIS

A kokarin da take yi na inganta ayyukan samar da fasfo ga dimbin masu nema da ke zaune a Kano da kewaye, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta kaddamar da Katafariyar Cibiyar Samar da Fasfo da za ta rika aiki ga ofisoshin fasfo na Jigawa, Katsina da kuma Dawakin Kudu da ke Kanon.

Da yake kaddamar da katafariyar cibiyar a ranar Laraba 11 ga Janairun 2023, Gwamna Abdullahi Umar na Jihar Kano ya taya NIS murna bisa dimbin nasarorin da take samu musamman kasancewarta ta farko da ta fara samar da sabon ingantaccen fasfo na zamani a duk fadin yankin Afirka.

Gwamnan wanda Kwamishinan Kasafin Kudi, Alhaji Danazumi Grazo ya wakilta ya jinjina wa NIS bisa kafa cibiyar a cikin Kano mai dimbin tarihi, yana mai cewa, ya yi amanna, zabar Kano da aka yi wajen kafa cibiyar ba zai rasa nasaba da yanayin zaman lafiya da ake mora a jihar ba.

A jawabinsa, Babban Shugaban NIS, Isah Jere Idris, MFR, ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, ana samun ci gaba a shirin sauya fasalin fasfo da ake yi a halin yanzu, musannam kan tsarin yadda za a yi saurin gane waɗanda suka shigo daga sassa daban-daban na duniya.

Shugaban ya ce, yanzu haka a Kano, sun ƙaddamar da cibiyar aikin yin e-Passport da aka inganta na zamani, kuma suna ci gaba da faɗaɗawa zuwa sauran wurare.
Wanda ya wakilce shi a wajen taron, ACG Sadat Hassan, ya ce, ya yi matuƙar farin ciki da jin irin ci gaban da ake samu a dukkan sassan yin fasfo ɗin a dukkan faɗin ƙasar nan, wanda ya nuna yadda mutanenmu ke bayar da cikakken haɗin kai. “Mun shirya za mu shafe mako biyu cif muna yin wannan aikin daga yanzu har zuwa ranar 21 ga wannan watan na Janairu, wanda kuma a wannan lokacin ne za kamala shirin.”

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

  • Tinubu Ne Kadai Zai Iya Magance Rashin Tsaro Da Tabarbarewar Tattalin Arziki – Buhari 

Ya kuma ƙara da cewa NIS za ta ci gaba da bayar da fasfo ɗin a tsakanin mako uku zuwa mako shida, kana iya tura bayananka, musamman ga mutanen da ba su da matsala wajen tura bayanan ko kuma a rubuta takardar buƙata.Ya ƙara faɗa da babbar murya cewa NIN na daga cikin shika-shikan yin fasfo wanda kuma dole a tabbatar da cewa, bayanan da ke cikinsu ba su saɓa ba.

“Muna ƙara samun ci gaba ne don haka muke kira ga masu neman fasfo ɗin su guji yin bayanan ƙarya su tabbatar sun yi bayanan da kansu kuma sun biya dukkan kuɗaɗen da hannunsu , za su shigar da bayanansu ta hanyar shiga wannan adireshi, passport.immigration.goɓ.ng.Za kuma mu ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen dukkan matsalolin da za a ci karo da su.”

Haka kuma ya ce, zai yi amfani da wannan damar wajen gode wa jama’a kan cikakken goyon bayan da suke samu a wajensu. Haka kuma ya nuna cewa, yanzu haka dai NIS ba ta ɗaukar mutane, kuma duk lokacin da za ta ɗauka za ta sanar a kafafe yaɗa labarai, wato lokacin da muka samu amincewar gwamnatin tarayya.

NIS

Shugaban hukumar, Jere ya tabbatar da cewa, jami’an hukumar a tsaye suke ƙyam wajen ganin ganin sun gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada, saboda haka ne ne ma y ace kullun suke ƙara samun ci gaba wajen gudanar da ayyukansu musamman a ɓangaren gudanar da fasfo da ɓangaren tsaro da samun walwala.

Saboda haka ne ma NIS take son isar da saƙonta ga dukkan jama’a cewa akwai fasfo guda 110,000 da masu su ba su zo sun karɓa ba a jihohi 36 da ke ƙasar nan da Abuja. Saboda haka, shugaban hukumar ya raba manyan jami’an hukumar tun daga kan mataimakinsa zuwa shiyya-shiyya domin ganin an tafiyar ta tsarin bayar da fasfo ɗin kamar yadda ya kamata.

Saboda haka ne ma ake shawartar ‘yan Nijeriya waɗanda suka yi fasfo ɗin ba su karɓa ba su je ofishin yin fasfo na NIS ɗin su duba nasu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro
Manyan Labarai

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina
Labarai

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Next Post
An Yi Shawarwari Karo Na 8 Bisa Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU

An Yi Shawarwari Karo Na 8 Bisa Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
NIS

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.