Connect with us

LABARAI

NIS Za Ta Ci Gaba Da Bayar Da Fasfo Daga Litinin Mai Zuwa

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta bayyana jadawalin karbar fasfo da aka riga aka yi da kuma lokutan da za ta fara karbar bukatar masu neman a yi musu sababbi.
A wata sanarwar manema labarai da Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya fitar ta hannun Jami’in yada labaran hukumar, DCI Sunday James, hukumar ta bayyana cewa za ta fara bayar da fasfon ne a ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020, sakamakon sassauta dokar hana fita da Gwamnatin Tarayya za ta yi sannu a hankali a Legas da Abuja.
Kamar yadda sanarwar ta nuna, mutanen da suka riga suka gabatar da bukatar yin fasfo za su garzaya “shalkwatar hukumar da ke Abuja da kuma daukacin ofisoshin bayar da fasfo da ke sassan kasar nan daga ranar 4 zuwa 15 ga watan Mayun 2020, amma ban da a jihohin da ba su sassauta dokar hana fita ba dangane da cutar Korona. Masu neman fasfo da aka aika wa sakon waya na SMS ne kadai ake bukatar su je su amsa a ranakun da aka ambata.
“A ranar 18 ga Mayun 2020, za a fara karbar bukatar masu neman a yi musu ingantattun sababbin fasfo a ofisoshin hukumar da suke bayarwa kamar haka: shalkwatarta ta Abuja, ofishinta na Ikoyi, Alausa, Kano da kuma Fatakwal.
“A ranar 25 ga Mayun 2020, dukkan ofisoshin bayar da fasfo za su fara aiki tare da bin matakan kiyaye lafiya da suka hada da; barin tazara a tsakanin mutane, sanya takunkumin riga-kafi da kuma amfani da sinadarin tsaftace hannu”.
NIS ta bayyana cewa za a gudanar da dukkan ayyukan fasfon ne daidai da ka’idojin da Hukumar Shawo Kan Annobar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta shimfida.
Shugaban NIS, Muhammad Babandede ya jaddada bukatar da ake wa Jami’an hukumar da ke aikin fasfo da mutane masu bukatar a yi musu, su tabbatar da bin ka’idojin da NCDC ta shimfida domin kauce wa yada cutar Korona a tsakanin jama’a.
Advertisement

labarai