NIS Za Ta Kori Duk Jami’in Da Aka Kama Yana Cin Amanar Aiki – Babandede

Kwantirola Janar (CG) na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Muhammad Babandede, ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta yi wata-wata ba wajen sallamar duk wani jami’in da aka kama yana cin amanar aikin da ƙasa ta ɗora masa.

Babandedewanda ya ba da wannan gargaɗin yayin da ke ganawa da jami’an NIS reshen hukumar da ke Katsina. Ya ce, yana daga cikin aikinsu tabbatar da bai wa ƙasa kariya ta dukkanin iyakokinta, don haka amsar cin hanci don kauce wa ƙa’idar aiki sam ba abin lamunta ba ne.

“Aiki ne da ke rataye a wuyayenmu, mu tabbatar da kare iyakokin ƙasa ta sama ko ƙasa. Matsalolin da suke jibge a iyakokin ta hanyoyin ƙasa dole ne mu canza taku. Daga yanzu babu wani cin amanar aiki ko kauce wa ƙa’idar ayyukan da suke gaban jami’ai.”
A cewarsa, hukumar tana ɗaukan dukkanin nauyin tabbatar da walwala da jin daɗin jami’anta tare da samar musu da ƙarin girma a kai a kai, don haka babu wani dalilin cin amanar aiki ga kowani jami’a.
“Wasu jami’an suna matuƙar kauce wa ƙa’ida a wuraren da aka tura su aiki na amsar cin hanci daga wajen al’umma a shigayen bincike,” kamar yadda ya shaida.
Shugaban ya kuma shaida cewar sun samu rahotonni da daman gaske da suke nuna yadda mafi yawan jami’ai ke amsar cin hanci a shingayen bincike wanda ya nuna cewa sam ba za su ci gaba da zura ido hakan na ci gaba da faruwa ba.
“NIS a ƙarƙashin jagorancina ba za ta taɓa lamuntar cin amanar aiki ba, saboda da zarar ka ci amanar wurin aikinka, ka ci amanar tsaron ƙasa ne baki ɗaya,” ya bayyana.
“Wasu daga cikinku sun kasance a wuraren ayyukan da aka turansu suna abubuwan kamar ba na masu hankali ba. Shi ya sa suke ƙarɓar cin hanci.
” Duk wanda na kama ya je ya yi magana da wani Sanata ko mamba a majalisa da sunan kamun ƙafa dangane da wata ta’asa da yayi , to fa babu abin da hakan zai haifar illa kora daga aiki.
“Ta wajen wasunku ne masu shiga ko fita ke zuwa inda kuke amsar kuɗi a hannunsu. To abin ya isa haka gaba ɗaya,” in ji shi. Ya yi gargaɗi da jan kunne yana mai cewa bai dace tsaron ƙasa ya cigaba da shiga garari sakamakon aikin ashssha na wasu jami’ai ba.
Ya tunatar da su cewa ayyukansu na da matuƙar muhimmanci don haka su daina cin amanar aiki a wuraren aka tura su.

Exit mobile version