Nishadi Da Soyayya A Tarihi: Labarin Wani Talaka Da Sarakuna Biyu

Tare da Huzaifa Dokaji arabiandokaji@gmail.com   08135353532

Idan akai zancen Daular Musulmi, yawancin mutane na kawo tsattsauran ra’ayin bauta da rashin more jin dadin rayuwa. Shin haka abin yake ko kuma dai rashin sani ne, wai kaza ta kwana akan dami? Kusan duka daulolin Musulmi da suka wanzu, cike suke da tarihi na soyayya da nishadi da abubuwa na dadin rayuwa. Ba wai soyayya irin ta su Rabi’atul Adawiyya ko Jalaludden Rumi ba, a’a soyayya ta mutan duniya. Misali, mai karatu ya ayyana ga mutum a zaune a lambu, iskar yamma na kada shi, ya dauka wanka, ya sha kaya da ba yamutsi tattare da su, ga ruwan lemo yana sha, ga jama’arsa sun kewaye shi suna sauraran bisar sarewar da yake yana yabon abar sonsa.

Mai karatu na san ka tafi akan lallai wannan mutum da aka fasalta a sama, dan gaye ne, kila ma baturen wannan zamani. Sai dai kash, wannan dan gaye da aka fasalta ba kowa bane face Abul Hassan Ali Ibn Nafi (789–857) wanda aka fi sani da suna Ibn Ziryab, wato shahararren dan gayen nan da ya rayu a daular Andalus a karni na takwas. Wannan bawan Allah dai wani abun ban sha’awa, baki ne. Kamar yadda mawaka suke sunnanta wanka da kwalliya idan suka yi ta a wakokinsu, ko yan kwallon kafa, haka shigar Ibn Ziryab take zama yayi idan ya yi a kasar Andalus. Ba wai iya saka kaya da zaman majalisar nishadi da yamma ba kawai, shi ne ya fara sunnanta goge baki sau biyu a rana a Turai. Shi ne kuma ya fito da tsarin saka sutura na mai nauyi ga sanda za a sa, mara nauyi ma ga sanda ya dace a saka.

Ibn Ziryab shi ne ya fara sunnanta cin abinci sau uku (3) a rana. Kafin zamansu tare da Musulmi a Andalus, Turawa basu da wani tsayayyen tsari na cin abinci. Ibn Ziryab shi ne ya kambama cin abinci mara nauyi da safe, mai nauyi da rana da kuma mara nauyi da dare. Wannan tsari na cin abinci har yau yana da tasiri kwarai , domin kusan dukkan al’umman da suka samu Turawa a tsakaninsu sun dauke ta. Ko da yake wannan dabi’a ta tsafta tasiri ne na Musulmi ga duniya, sai dai fa yanzu akwai alamar basa damuwa da ita yanda ya kamata. Kana iya kwatanta shi da sarauniyar Ingila Bictoria, wacce aka ce a zamaninta ba mai tsaftar ta a Ingila. Ance saboda tsabar tsaftarta tana yin wanka sau biyu a wata, ko ta yi datti ko bata yi ba! Ibn Ziryab a rana yace yana da kyau ayi wanka sau biyu.

Daga kwalliya bari mu zarce filin soyayya. Da aka ce soyayya, shin ta Sufantaka mai karatu ya kawo a ransa? To fa mu ba nan muka dosa ba. Yau alkamin namu birnin masoya ya nufa. Ba wai fa a wannan zamani ne aka fara soyayya ta kirki, ta tsiya, yaudara da kuma sa hawaye ba! An dade ana ruwa kasa tana shanyewa. Bari mu bude da labarin Abdurrahman III (912–961), Sarkin Andalus, da matarsa abar son sa, Saruniya Zahra. Farin cikin dukkan masoyi shi ne samun masoyiyar da zasu dinga zuba gasar furtawa da nunawa juna soyayya da kulawa. Ayi musayar baitukan soyayya, a kalli juna a jika kunci da hawayen farin ciki, a rubuta wasiku masu dauke da kalamai masu kashe zuciya. Sarki Abdurrahman III ya samu wannan duka a gun sarauniyarsa Zahra.

Ba wai iya soyayya ba, hatta a harkar mulki, Sarki Abdurrahman III da Sarauniya Zahra yake shawara, ko shari’a zai yi tana cikin wadanda yake saurara. Idan zai yanke wani hukunci mai tsauri, kamar yanke hannu ko kisa, ita take karfafa masa gwiwa akan dole ne fa ya tashi tsaye ya sauke hakki, dukkan abinda yake daidai a yi shi. Wata rana Sarki Abdurrahman III ya tashi da niyyar sai ya barwa duniya wani labari da zata dorar akan wannan so mara misaltuwa da yake wa matarsa. Shin me zai yi shi kuwa? Shawararsa ta tsaya akan zai gina sabon birni, wanda duk duniya babu irinsa! Nan da nan aka fara aiki, akai gini irin wanda ko a wannan zamanin na fita kunya ne. A wannan gari an gina fada, wadda ba irinta. Wani abin sha’awa shi ne, kaf an rufe kasan, ba kasa, an kuma fitar da tituna an saka fitilu. An kawata gine-ginen da gilasai da irin fanfon nan mai fesar da ruwa (fountain) da kuma gidajen wanka samfurin zamani.

Sarki Abdurrahman III ya kira wannan fada da suna “Madinatuz-Zahra, wato ‘Birnin Zahra.’ Fadarsa da ya gina a cikin wanan sabon birni nasa ta zama fada da ba irinta kaf a duniyar Turai a wancan lokacin. Dauloli kullun a cikin turo jakadu da aiko wasiku suke. Sai dai fa duk da wannan kashe kudi da akai wajen gina wannan daula, babu wani abu da ya rage nata da zamu iya gani. Yake-yake da rashin damuwa da adana kayan tarihi irin na Musulmi yasa san abinda ya rage ba komai bane face kufai. Lokacin da wannan daula ta Afirka take da wannan alatu, ba wai iya ci gaba ba kawai tafi sauran manyan biranen Turai ba har da jama’a. A wannan lokaci gaba daya jama’ar Landan basu fi mutum dubu goma ba, in da wannan gari ke dauke da mutum sama da dubu dari biyu.

Daga Andalus bari mu garzaya kasar Indiya birnin Sarki Shahab-ud-din Muhammad Khurram (1592–1666) wanda aka fi sani da Shah Jahan, mijin sarauniya Arjumand Banu Begum, wadda aka fi sani da Mumtaz Mahal. Sarki Shah Jahan na cikin jerin sarakuna Musulmi da akai a Indiya. Sarki ne mai tsayyyen iko wanda baya wasa, ba kuma ya daukan raini. Wannan sarki kamar yanda muka fada yana da wata mata da yake matukar kauna. Kana taka Allah ma tasa, wannan sarauniya ta zo haihuwa kwatsam sai ta rasu. Rasuwar Mumtaz Mahal ya tada hankalin wannan sarki kwarai domin harkar mulkinsa ma kaf a hannunta take. Ya dimaita ya kasa sukuni, ya shiga tunanin me zai yi ya barwa duniya shaidar sonnda yake wa wannan mata tasa. Sarki Shah Jahan yayi shawarar gina wani guri na musamman da zai killace kabarin wannan mata tasa. Ya yu tura jama’arsa su shiga duniya, su nemo masa magina da masu ado.

Shah Jahan ya bada umarnin cewa duk mutumin da aka dauko da za ai wannan aiki da shi, a tabbatar ba mai kwarewarsa a wannan fannin. Wato misali, idan aka dauko mai fenti, to a tabbatar a duniya yafi kowa iya fenti. Haka kuwa akai, aka hada mashahuran ma’aikata suka dukufa, ba dare ba rana. Wannan gini da akai har yanzu yana nan a kasar Indiya. Shi ne ginin da ake kira ‘Taj Mahal’, wanda za a ga ana nuna shi a finafinan Indiya, da wani dan dogon tafki na ruwa a gabansa, da fararen kubbobi a samansa da tattabaru. Da wahala a kalli fim din Indiya ba’a gan shi ba. Kabarin matar na daidai saitin babbar kubbar. Sai dai fa wannan abu da Shah Jahan yayi na karrama matacciyar matarsa da koke-koke da surutai da ya dinga yi, ya bar baya da kura domin dansa na cikinsa yayi amfani da hakan wajen gamsar da jama’a cewa mahaifin nasa fa ya samu matsala. Ya tumbuke shi daga kujerar mulki ya sa shi a turu.

Shah Jahan ya rasu a cikin wannn hali, inda kuma aka binne shi a wannan shigafa da ya ginawa kabarin matarsa. Kabarinsa na saitin karamar kubbar, gefen na matarsa, abar sonsa, Sarauniya Bibi Bilkis Mahal. Idan muka duba wadannan labarai, zamu ga cewa soyayya ta taka rawa kwarai wajen ci gaban tarihi da kuma sauye-sauye a harkar siyasar duniya. Mun kuma ga cewa, ko da yake a yau kasar Andalus an cire ta daga Afirka amman da a ciki take. Mun kuma ga yanda soyayya tasa wani daga cikin sarakunan wannan daula ta Afrika ya gina birnin da ba irinsa a duniya a lokacin saboda tasirin soyayya. A duk sanda akace da kai babban yaro saboda tsafta ko ado sai ka tuno da Ibn Ziryab. Idan kuma kaji soyayya ta hana ka sukuni, ka yi wata bajinta saboda ita ko kuma wata masifa ta same ka saboda ita, sai ka tuna da Sarki Abdurrrahman na Andalus da Shah Jahan na Indiya

 

Exit mobile version