NITDA Tayi Gargadi Game Da Bairos Mai Boye Kayyakin Komputa ‘IGBM Ransomware’

NITDA

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) ta gargadi ’yan Nijeriya da su yi hattara da IGBM Ransomware, wani Bairos da ke boye samun bayanan komfuta, kamar takardu, hotuna, da bidiyo.

 

Uwargida Hadiza Umar, shugabar sashen hulda da kasashen waje ta hukumar, ta yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

“Bairos din yana lalata komfuta ta hanyar boye abubuwan komfuta kamar hoto, waka bidiyo, takardu da dai sauransu, Bairos din akarshen sunanshi yana zuwa da ‘IGBM’ bayan ya boye kayayyakin komfutar sai ya nema abiya kudi ta hanyar manhajar Bitcoin don samun damar dawo da abubuwan da ya boye”

Ta ce crypto-birus na iya yaduwa ta hanyar yanar gizo (internet), da satar software, da sakonnin imel na wasiku, da lalatattun software, da sabunta manhajojin karya, da kuma tallace-tallace na yanar gizo na yaudara.

 

“Manufar Bairos IGBM ransomware ita ce bincika tsarin kwamfutarka don neman wasu ajiyarka mai matukar amfani ta hanyar amfani da fasahar (RSA) mai zaman kanta. Da zarar Bairos din ya kulle abunda yake nema sai ya fara sacewa da tura muhimman ajiyarka zuwa wata ma’ajjya tw hanyar amfani da Command.Ede

 

“Hakanan yana hana wadanda abin ya shafa su maido da kwafin fayil dinsu har sai sun biya wani kudi.

” sannan kuma, Bairos din yana lalata hanyar shiga yanar gizo, ta yadda bazaka iya tambayar Google ba kan yadda zaka mayar da kayayyakin ka. ” in ji ta.

 

Ta bukaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar da adana bayanansu na  yau da kullum da dukka muhimman bayanai a wata ma’ajiya ta musamman don shirin ko ta baci.

 

“su kuma dunga yin amfani da wasu manhajoji don kula da komfuta da da zata taimaka wajen fita daga tsarin da baka amfani da shi.

 

“Kuma ta bukaci mutane da au dinga amfani da software mai rigakafi ga Bairos.

 

“Kada ku bi hanyoyin yanar gizon da ba a amince da su ba, wadanda ake turawa cikin email,” in ji ta. Akwai masu yin hakan, su kirkiri Bairos sannan su saida maka da maganin rigakafin Bairos din. Ta bayyana hakan a matsayin wata hanya ce ta damar da kudi ga tsarin kasuwanci ba bisa ka’ida ba, don haka ya kamata ‘yan kasa su guji hakan.

Exit mobile version