Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tabbatar da cewa dan wasanta, Eddie Nketiah, ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar kakar wasa biyar, domin ci gaba da buga mata wasa.
Daman dai kwantiragin dan wasan zai kare ne karshen watan nan, wanda ya buga wasanni 92 da cin kwallo 23, tun bayan da ya fara buga wasa a kungiyar a shekarar 2017.
- Chelsea Tana Tattaunawa da Manchester City Kan Sayalen Sterling
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Hadari Da Tsawa Na Kwanaki 3 Daga Ranar Litinin
Ya taka rawar gani daga karshen kakar da aka kammala a Arsenal, wanda ya buga wasa takwas da saka kwallo biyar.
Nketiah dai zai dinga saka riga mai lamba 14, bayan da ya yi amfani da mai lamba 30 a baya kuma ya fara da cin kungiyar Norwich City kwallo biyu a Caraboa Cup a wasansa na farko a 2017, yana cikin jerin ‘yan wasan Arsenal da suka lashe FA Cup da Community Shield a 2020.
Dan wasan shi ne kan gaba a tawagar matasan Ingila ‘yan kasa da shekara 21, mai kwallo 16 a raga a fafatawa 17 da ya yi mata sannan shi ne kyaftin a tawagar Ingila ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 da ta lashe kofin Nahiyar Turai na matasa a 2021.