Kungiyoyin Kwadago da suka hada da kungiyar kwadago ta Njeriya NLC da Kungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC) sun kammala gangamin hada kan mambobinsu da kungiyoyinsu domin shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar nan daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba, 2023.
Lamarin ya biyo bayan kauracewa taron da gwamnatin tarayya ta shirya a ranar Juma’a a matsayin mataki na karshe na dakile yajin aikin.
- Tinubu Ya Jaddada Aniyar Magance Rashin Tsaro Da Talauci A Nijeriya
- Danbarwar Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ta Dawo
Tuni dai kungiyoyin kwadagon suka tsaya tsayin daka na cewa babu ja da baya kan shirin yajin aikin.
Ƙungiyoyin guda biyu, wadanda suka sanar da fara yajin aikin bayan wani taron manema labarai na hadin gwiwa a ranar Talata a Abuja, sun ce yajin aikin ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen magance wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da sauran munanan manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Sun kuma zargi gwamnatin kasar na. da kin shiga tattaunawa da su duk da wa’adin kwanaki 21 da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka yi a ranakun 5 da 6 ga watan Satumba.