Kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Ogun, ta bai wa gwaman jihar Dapo Abiodun wa’adin kwana bakwai na ya biya bukatun ma’aikatan jihar ko kuma su tsunduma a cikin yajin aiki.
NLC ta kuma soki Abiodun kan yankar albashin ma’aikatan Jihar har na tsawon watanni 21 da kuma kin biyansu kudadensu na hutu har na tsawon shekaru takwas, tare da karya dokar biyan kudaden fansho ta jihar ta shekarar 2013 da aka sabunta.
- Dakarun Sojin Nijeriya Sun Kama Bama-Bamai Da Alburusai A Jihar Kuros Riba
- Kotu Ta Daure Wani Matashi Wata Daya Kan Satar Tukunyar Miya
Korafin na kungiyar na kunshe cikin wasikar da Shugabanta, Emmanuel Bankole da Shugaban kungiyar TUC Akeem Lasisi da kuma Shugaban kwanitin JNC Isa Olude suka rattaba wa hannu.
A cewar shugabannin, walwala da kuma jin dadin ma’aikatan Gwamnatin jihar na cikin mawuyacin hali a cikin shekaru uku da suka wuce.
Sun sanar da cewa, a ranar 7 ga watan Yunin 2022 sun tura wasika zuwa ga Gwamnatin jihar da ke nuni da irin halin da ma’aikatan ke ciki tare da gabatar da yin kiran gaggawa don a zauna a tattuna da Gwamnatin don a samar da mafita.