Nnamdi Kanu: Gwamnati Ta Sanya dokar Ta-Baci A Abia

Daga Musa Muhammad, Abuja

A halin da ake ciki dai Gwamnatin jihar Abia ta sanya dokar ta-baci a jihar sakamakon barkewar rikici tsakanin Sojoji Nijeriya da matasa magoya bayan Nnamdi Kanu ta IPOB.

Gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu ya sanar da sanya wannan doka ta kwana uku, inda ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da biyayya ga tsarin mulkin kasar nan. Ya ce wannan doka za ta kasance ne daga karfe 6 na yammacin jiya Talara zuwa 14 ga wannan wata na Satumba.

Sanya doka dai ya biyo bayan dauki ba dadin da aka kwashe kwanaki biyu ne ana yi tsakanin sojojin da matasan kungiyar ta IPOB, sakamakon sintirin da sojojin ke yi, wanda kuma wannan sintiri ya kai su har bangaren gidan Shugaban kungiyar.

Lauyan Kanu ya yi korafin cewa a halin da ak ciki sojojin suna tsare da wanda yake karewa a gidansa a Afaraukwu, wajen Umuahia, babban birnin jihar.

A wata sabuwa kuma, labarai sun yadu jiya cewa sojojin sun je sakatariyar ‘yan jarida NUJ na babban  birnin jihar, inda suka lallasa wasu ‘yan jarida da dama, kuma suka tarwatsa masu kayan aiki. Amma rundunar sojojin ta karyata wannan labari.

Cikin wata sanarwa da Mataimakin Kakakin runduna ta 14, Manjo Oyegoke Badamosi ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa wannan labari ba gaskiya ba ne, “abin da ya faru shi ne, wasu sojoji da ke sintirin ta bangaren da sakatariyar ‘yan jaridar, NUJ ta ke, suna wucewa sai suka lura da cewa wasu na daukarsu hoto, abin takaici sai suka kwace, tare da farfasa masu abubuwan, wadanda suka hada da iPad da wayoyi guda biyu. bayan bincike sai aka gano ashe abin na ‘yan jarida ne.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, amma daga bisani Kwamandan rundunar ta 14 , da maitamakin Kakakin Runduna ta 82 sun shiga maganar, “kuma sojojin da aka kama da hannu a wannan abin, za a hukuntasu,” in ji sanarwar.

Exit mobile version