Dakta Sheriff Almuhajir
Kamar yadda aka saba, satin da ya gabata ya zo wa da ‘yan Nijeriya da sabon maudu’i wanda ya rinjayi yawancin jaridu da kafafen sadarwa na zamani. Labarin taƙaddamar da ta ɓarke a ɗaya daga cikin masana’antu ma fi daraja a Nijeriya watau NNPC. Sakamakon wasiƙa da ƙaramin ministan man fetur Ibe Kachikwu ya aike wa Shugaba Buhari, sannan aka sake ta ga ‘yan jaridu har ta bayyana ga ‘yan Nijeriya.
Na zaɓi in yi shiru akan wannan magana har sai na samu tattaunawa da mutanen da na ke da amana da su kuma suke cikin jagorancin wannan ma’aikata, saboda wasu lokuta ‘yan jaridu ma na shigar da ra’ayinsu ko makarkatarsu cikin rahotanni. Bayan tattaunawa mai tsawo na yi niyyar shigo da wannan batu cikin rubuce-rubucena, domin sanar da ‘yan’uwa na halin da ake ciki akan nazarin wasu ma’aikatan cikin gidan NNPC.
Na gane cewa fahimtar waɗannan mutane da halayyarsu yana da muhimmanci wajen fahimtar abunda ya afku. Farko wanene Kachikwu, kuma wanene Maikanti Baru?
Kachikwu, ɗaya ne cikin jagororin kamfanin mai na Eɗɗon Mobil, kamfanin da ya daɗe yana tatsowa da tace Mai a Nijeriya, bayan samun nasarar Shugaba Buhari aka ba shi shawara ya ɗauko Kachikwu sakamakon gogewarsa a wannan fannin. Bayan ɗarewarsa an samu ci gaba wajen kawo sauye-sauyen gudanarwa a NNPC, amma duk da haka, ƙungiyoyin ma’aikata sun zarge shi da shigar da son rai wajen kawo abokanan aikinsa na baya da maye gurbin ma’aikatan NNPC. Sannan da ragewa nagartattun ma’aikatan matsayi da ayyukan su.
Misali shi ne; ya samu Maikanti Baru a matakin Group Eɗecutiɓe Director (GED), Amma saboda wasu dalilai da har yanzu ba a gane su ba, sai ya ma cire shi daga uwar ma’aikatan NNPC zuwa Ministry, ya mai da shi matsayin mai bashi shawara a harkar Gas. Wannan ba ƙaramin ci baya ba ne ga mutumin da ya kai matakin ofishin mutum na biyu a dawo da shi aikin ofishin mutum na biyar.
A wannan zamani na Kachikwu dai ‘yan Nijeriya suka sha baƙar wahalar samun man fetur da ya tilastawa ‘yan ƙasa amincewa da ƙarin tsadar man fetur daga 87 zuwa 145. Matakin da ya jawo wa Shugaba Buhari fushin ‘yan Nijeriya baki ɗaya. Sannan aka yi ta yunƙurin sayar da haƙar man fetur ga ‘yan’uwa da abokan Kachikwu kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Daga farko an yi tsammani Kachikwu zai samu muƙamin babban Ministan albarkatun Mai, Amma sakamakon zarge-zarge da suka yawaita, EFCC suka shiga binciko abubuwa da dama, sai shugaban ƙasa ya sauya tunaninsa ya maida shi ƙaramin Ministan Mai, sannan ya raba shi da jagorancin NNPC. Abunda zai tabbatar maka da cewa akwai matsalar da ta haifar da hakan, shi ne zaƙulo Maikanti Baru wanda shi ne babban abokin adawar Kachikwu a NNPC.
Maikanti Kachalla Baru:
Maikanti kamar yadda abokan aikinsa suka tabbatar, a tarihin shekarun aikinsa da NNPC ba a taɓa samunsa da karya doka ba, balle zargin almundahana, saboda nagartarsa, tun lokacin Umaru Musa ake tsammanin za a ba shi muƙamin GMD, amma Allah bai nufa ba. Shi kuma Jonathan dama hanyar su ba ta zo ɗaya ba, saboda haka ko nemo shi ba a yi ba, duk da haka sunansa ya sha zuwa gabansu akan dacewarsa da wannan muƙamin.
Bayan binciken da aka soma akan Kachikwu, makusanta Buhari suka ba shi shawara cewa Maikanti mutum ne da suke gani in dai aka ba shi wannan sashe, to al’amura za su daidaita. Kuma da gaske bayan an ba shi wannan hukuma ta samu ci gaba mai yawa. Ma fi girman su shi ne tsaftace hanyoyin da ake bi wajen yin badaƙala a shekarun baya. Da kuma inganta ayyukan Mai ta yadda kowa ya ji tsit tamkar Man fetur bai kasance abun damuwa ba.
Me Ya Faru A NNPC
Buhari Shugaba ne mai gaskiya, amma wasu na zargin yana da sakaci wajen ladabtar da mutanen da ke da kusanci da shi. Kila wannan ɗabi’a ce ta sanya bai sallami Kachikwu ba, amma sai ya rufe masa aofa kuma ya bawa Baru damar isar da saƙon hukumar NNPC kai tsaye gare shi matsayin babban Ministan albarkatun Mai da kuma shugaban ƙasa. Wannan yanayi bai yi wa Kachikwu daɗi ba, amma zahiri ya nuna an yi hakan ne saboda halayen da ya yi a baya.
Saboda haka sai Baru ya fara aikin tsaftace ma’aikatar daga mutanen da Kachikwu ya shigo da su ya ciccire baƙin ma’aikatan daga aikinsu, ya sanya tsofin ma’aikatan NNPC. Baru ya fara bi ɗaya bayan ɗaya yana sauyi, ana ba su “acting” riƙon ƙwarya kafin Ministan Mai kuma shugaban ƙasa ya dawo. Shugaban ƙasa na dawo wa Baru ya miƙa ma sa takarda kuma ya sa hannu, daga nan kowa ya samu takardarsa ta dindindin.
Zargi na biyu da Kachikwu ya yi wa Maikanti shi ne bayar da kwangilar da ta kai dala miliyan 25 ba tare da sanin Minista ko sa hanun Majalisar Zartaswa ba. A takardar da NNPC ta gabatar ga ‘yan jarida a ta nuna cewa Kachikwu dole ya shiga cikin ɗayan biyu; imma zunzurutun rufewar idanu da ta sa ya mance ƙa’idoji da tsare-tsare, ko kuma ainihi bai laƙanci aikin NNPC kamar yadda ake tsammani ba.
Daga ƙarshe dai, ‘yan Nijeriya sun sanya idanu domin ganin matakin da Shugaba Buhari zai ɗauka akan wannan dambarwa tsakanin Ibe Kachikwu da Maikanti Baru.
Almuhajir Malami ne a Jami’ar Yobe.
Za a iya samun sa a sheriffalmuhajir@gmail.com