A wani abun da ake kallo a matsayin maida martani ga rage farashin farko da matatar Mai ta Dangote ta yi, kamfanin kula da albarkatun mai ta kasa (NNPCL), ya rage farashin litar mai daga naira 945 zuwa naira 860 a Legas da kuma naira 865 a Abuja.
Tuni gidajen man NNPC a sassa daban-daban musamman a Ori-Oke, Egbe, Ikoyi, da na kan hanyar Ikorodu a Legas suka sauya sabon farashi, yayin da haka zancen yake a gidajen man NNPC a Abuja da suka hada da Lugbe da Ketampe.
- Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
- Ƴar Majalisar Dattawa Natasha Akpoti Na Fuskantar Dakatarwar Wata Shida
Su ma gidajen mai masu zaman kansu da suke karkashin kungiyar dillalan mai ta IPMAN sun ce tuni mambobinsu suka rage farashin litar mai duk kuwa da cewa man da suke da su a halin yanzu sun saye su ne a kan tsohon farashi mai da tsada, domin su ci gaba da kasancewa cikin gasar cinikin mai.
Ko da yake kamfanin NNPCL dai bai fito a hukumance ya fadi dalilin rage farashin litar mai din ba, amma ana ganin kamar hakan ya biyo bayan yadda ‘yan Nijeriya ke zaben gidajen mai masu sauki domin sayen mai da kuma halin matsin da jama’a kasa ke fuskanta.
Wani kwararren masani kan makamashi, Wunmi Iledare, ya soki matatar Dangote da NNPCL kan kokuwar rage farashin, yana mai cewa ba ragewa ba matsalar dorewar saukin farashin shi ne abun da jama’an kasa ke da bukata a halin yanzu.
“NNPC na amfani da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje domin yin gogayya da matatar Dangote, a maimakon ta dukufa amfani da matatunta na mai da suke cikin kasar nan. Wannan lamarin na shafan dorewar musayar kasuwanci kuma zai kara janyo damuwowi ne kawai ga tattalin arzikin kasar nan,” Iledare ya shaida.
Wani masanin makamashi kuma shugaban NES, Farfesa Adeola Adenikinju, ya ce akwai bukatar hukumomi su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da wadatar mai da kuma saukinsa a kasuwanni.
Ya kuma lura da cewa akwai bukatar magance dakile gasar rashin adalci domin a samu yin ciniki sosai a tsakanin masu mai.
Mataimakin shugaban IPMAN, Hammed Fashola, ya nuna farin ciki da rage farashin litar mai, wanda ya yi nuni da cewa mafi yawan ‘yan Nijeriya da ita suka dogara.
Ya tabbatar da cewa dillalan mai da dama sun fara sayar da mai a gidajen mansu kan farashin mai rahusan duk kuwa da cewa sun sayi mai din a farashi mai tsada.
Fashola ya ce, “Yayin da NNPCL ke sayar da mai kan lita guda a naira 860 a gidajen manta, amma sabon farashin bai nuna haka ba, amma ana ta kokarin sabuntawa.”
Duk kokarin jin ta bakin mai magana da yawun NNPC, Femi Soneye, ya citura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp