NNPC Ya Samar Da Litar Fetur Biliyan 1.44 A Watan Janairu

NNPC

Kamfanin manfetur na kasa (NNPC), ya bayyana cewa, ya samar da lita biliyan 1.44 na manfetur a watan Janairu na shekarar 2021.

Adadin ya kai yawan adadin da ake samarwa a kowace rana na miliyan 46.30. Bayanin amfani da mai na watan Janairun ya sha bamban da na kimanin lita miliyan 70 na mai na yau da kullum.

Babban manajan kamfanin da rukunin hulda da jama’a, Dakta Kennie Obateru, a cikin wata sanarwa a jiya, ya ce, bayanan na kunshe ne a cikin watan Janairu na 2021 na rahoton kudi da ayyuka na NNPC, MFOR. Ya bayyana cewa, a bangaren iskar gas, an samar da jimillar cubic feet na biliyan 223.55 na gas a watan Janairu na shekarar 2021, wanda aka fassara zuwa matsakaicin samarwar da ake samu a kowace rana ta ‘7,220.22 mmscfd’.

“Yawan samar da iskar gas na 223.55BCF ya kuma nuna karuwar kashi 4.79 bisa dari kan abin da ake fitarwa a watan Disamba na shekarar 2020. Yawan samar da iskar gas a kowace rana ga tashoshin samar da iskar gas ya karu da kashi 2.38 bisa dari zuwa 836mmscfd, kwatankwacin samar da wutar na 3,415MW,” inji sanarwar.

Ya bayyana cewa, a tsakanin watan Janairun 2020 zuwa Janairu 2021, an samar da jimillar 2,973.01BCF na gas wanda ke wakiltar matsakaita na yau da kullum na 7,585.78 mmscfd a lokacin.

“Samun zamani zuwa yau daga hadin gwiwa JBs, yarjejeniyar rarraba kayana PSCs, da Kamfanin bunkasa manfetur na Nijeriya (NPDC), sun bayar da gudummawar kimanin kashi 65.20 bisa dari, kashi 19.97 da kuma kashi 14.83 bisa dari bisa ga jimlar samar da iskar gas. Daga cikin yawan iskar gas da aka fitar a watan Janairun 2021, jimlar 149.24BCF na gas an sayar da shi wanda ya kunshi 44.29BCF da 104.95BCF don kasuwannin cikin gida da na fitarwa bi da bi,” inji Obateru.

Exit mobile version