Jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Katsina ta yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ya sanya dokar ta baci a jihohi biyar na arewacin Nijeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina, Alhaji Sani Liti ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Katsina.
- Gwamnatin Ce Ta Harzuka Wanda Suka Sace Mu, Suka Fara Dukanmu -Wanda Ya Kubuta
- Zamu Hukunta Duk Wanda Ba Musulmin Ba Da Ya Sake Keta Harami – Saudiyya
Jahohin da jam’iyyar NNPP ta yi kira a kafa dokar ta baci sun hada da jihar Katsina da Zamfara da Kaduna da Neja da kuma Sakkwato.
Alhaji Sani Liti, ya kara da cewa yanayin da wadannan jihohi suke ciki na rashin tsaro ya kai intaha, saboda haka a duba lamarin domin ceto al’ummar da ke wadannan jihohi.
Shugaban jam’iyyar NNPP ya kara da cewa saka dokar na akalla watanni shida wanda hakan zai taimaka wajen bai wa gwamnatin tarayya damar É—aukar sha’anin tsaro da mahimmancin gaske.
“Haka kuma muna kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matasa miliyan daya aikin sa-kai sannan ta ba su horo na musamman domin tunkarar wannan matsala ta tsaro a wadannan jihohi masu fama da matsalar tsaro” in ji shi.
Haka kuma jam’iyyar NNPP ta kara da cewa yin haka zai kara ba gwamnatin tarayya damar kulle asusun ajiyar jihohin da aka kakaba wa dokar ta bacin domin yin amfani da kudaden jihohin wajen yin amfani da su a yaki matsalar tsaro.
Liti, ya ce idan har gwamantin tarayya bata dauki wannan mataki ba. Suna kira da babar murya ga majalisun jihohin da aka yi kira a kafa dokar ta baci akan su, da su fara gabatar da shirye-shiryen tsige gwamnonin wadannan jihohi.