Noma Na Iya Magance Matsalar Nijeriya -Kibiya

HONARABUL YUSUF ADO KIBIYA na ɗaya daga cikin manyan manoma da ake magana a yanzu a ƙasar nan, kuma Bafulatani ne wanda ya gaji noma da kiwo daga kaka da kakanni. Hakan ta sa shi sha’awar noma da karanta noma a makarantun zamani har zuwa Digiri a kan fannin noma, inda ya kai ga riƙe muƙamin kwamishinan Ma’aikatar gona ta Kano a tsakanin 99 zuwa 2003. Ya yi bayanin cewa, akwai Garba ABCD wani fitaccen mai faɗakar wa a rediyo Nijeriya Kaduna ya ziyarce su a gona a 1968 kuma ya yi bayani filla-filla a kan matsayin noma da amfaninsa da yadda mutane ya kamata su rungumi harkar da yadda hukuma ta dubi wasu al’amuran da suka shafi noma, wakilinmu MUSTAPHA IBRAHIM KANO ya samu zantawa da shi.

Da farko za mu so mu san da wa muke tare da shi?

Da sunan Ubangiji mai rahama mai jin ƙai, To kuna tare da Alhaji Yusuf Ado Kibiya kuma matsayina shi ne. ni dai manomi ne kuma ina noma abubuwa daban-daban, kamar shinkafa, gyaɗa masara dawa da sauransu kuma har ila yau ina harka samar da irin shuka na zamani kuma ina kiwo, shi ne matsayina a yanzu wato manomi.

To a matsayinka na babban manomi kuma ƙwararre, a yanzu mu na iya cewa damuna ta wuce kuma kaka ta fara shigo wa, yaya ka kalli damunar bana?

To a gaskiya damuna ta yi kyau, kuma damuna ce take da tsafta ba iska ba wani abu mara daɗi da ya faru a wannan damunan da za a ce ya kawo wa wannan damuna cikas da ya hana samun amfanin gona a yanzu dai maganar nan da nake da kai, saboda haka damuna ta yi kyau.

Kasancewar Noma da Kiwo kusan sune manyan sana’o’in Hausa Fulani dama sauran mutanan Arewa, a matsayinka na fitaccen ɗan siyasa yaushe ka shiga harkar Noma gadan-gadan?

To ai ni a gona aka haife ni, tunda ni kuma tun ina yaro na samu kaina a gidanmu ne ana Noma. Domin ba na iya mantawa ina tsammanin tun ina ɗan shekaru tara ba na iya mantawa wani fitaccen mai faɗakarwa a harkar Noma a gidan Radiyon Kaduna Alhaji Garba ABCD ya je ziyara can garinmu Kibiya a wannan lokacin ya same ni a Gona da Lauje a kan sankace ina yankan Dawa a wannan lokacin, har ya tambaye ni, “Yaro har da kai a wannan aiki!” (Ya yi dariya ya yi mamaki da ya gan ni ina aiki. Ya yi mamaki). Kuma ina tabbatar ma duk wani abu da ka sani na Noma ina yi, kuma ina yin kiwo na shanu da dai duk wani abu da manoma su ke yi na Noma ina yin shi ko na yi shi.

 

Ko za ka iya tuna lokacin da Alhaji Garba ABCD da Shata yake cewa ya kai ziyara  Kibiya ya same ka da Lauje a Sankace? Kuma Kadada nawa, ko Eka nawa ake samun dama a Noma a Shekara?

Shekarar dai ita ce 1967 zuwa 1968 a wannan lokaci ya zo mahaifata Kibiya. To kuma ka san Noma namu Noma ne na gadon gado kuma akwai noma daban-daban da muke yi. Akwai noman Rani, akwai na Damuna, na wannan lokaci misali. Kuma akwai noman Shinkafa akwai noman Masara da dai sauransu kamar yadda na gaya maka a baya. Saboda haka a dunƙule dai za ka ga akwai Noma mai wahala haka irin na su Shinkafa yanzu dai ka gan ta da idonka. Akwai kuma Noman gyaɗa, dawa, masara da sauransu saboda haka za ka ga akwai eka 28 wani gun 18 haka dai ga shi nan daban-daban a ƙiyasi ya iya haura eka 200 in ka haɗa da duka noman da muke a Rani da Damuna. Saboda haka sai ka ƙiyasta zai ba ka adadin ko kadada nawa kamar yadda ka yi tambaya.

Kasancewarka babba kuma fitaccen Manomi a Kano ko ma a Arewacin Nigeriya baki ɗaya, me ye gamsuwarka ko rashin gamsuwarka a kan yadda gwamnatin Tarayya da na Jahohi suke tafiyar da al’amurran Noma?

To gaskiya aikin noma yana da matsaloli masu yawa a cikinsa amma ni ina ganin kamata ya yi noma ya zama kamar sauran harkokin kasuwanci, ta yadda zai zauna da gindinsa, domin ta haka ne kawai za a samu dawwamammiyar alƙibila a harkar noma. Amma idan ka dubi yadda gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugabancin Muhammad Buhari ta ɗaura al’umma a wannan alƙibila ta noma za ka ga cewa an samu babbar nasara domin ko ba komai yanzu an samu tsai da da sata da ɓarna da kawar da ta’addanci da satar kuɗin banza duk yanzu wannan ta kau an sa wa mutane su je su yi noma.

To nasara ta biyu kuma da aka samu ita ce yadda aka samu taki a ba na bai yi irin mahaukaciyar tsadar nan ba ta yadda za a ce ga shi dubu goma dubu sha biyu ba a samu haka ba, wannan ma nasara ce. To amma ni a ra’ayina, ina ganin harkar taki ya kamata ta zama harkar kamfanoni masu zaman kansu. Ina ga idan ta za ma haka akwai gasa a tsakanin kamfanonin za a samu sauƙi. Abin dai da kawai ya kamata a yi shi ne, hukuma ta kula da tafi da al’amurran taki da ingancinsa da kuma ƙa’iduji da za a sa wa kamfanonin masu yin takin, hakan za ya sa harkar taki ta fita daga al’amurran siyasa in ka dubi gishirin miya, suga da makamantansu ai zuwa kasuwa kawai.

Sai kuma nasara ta uku da ake ƙoƙarin sarrafa shinkafa ta gida hakan abu ne mai kyau, domin wata rana sai ka ga an samu shinkafar Nijeriya a wasu ƙasashe, kamar ka ce Nigeria Rice.

In dai maganar Jahata ta Kano ce, domin a matsayina na wanda ya yi harkar noma tun ina sakandare na riƙe ƙungiyar Matasan Manoma ’yan makaranta, kuma na yi kwamishinan aikin gona a tsakanin 1999 zuwa 2003 a wannan lokacin, don haka na san abubuwa daban-daban a wannan harka. To idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin Kano ta farfaɗo da kamfanin sarrafa taki na KASKO da Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi ya kafa, farfaɗo da shi da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi to na san ko a wannan an yi ƙoƙari sosai kamar harkar samar da Iri da tura ’Ya’yan Fulani Turkiya don koyo bayen shanu, abu ne mai kyau da gwamnatin Kano ta yi.

Ranka ya daɗe akwai maganar gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin hana shigo da Shinkafa Ƙasar nan da kuma taƙaita shigo da ita ta ruwa kawai ya kake kallon wannan batu?

Shigo da shinkafa ta hanya ɗaya to kuma za ka ga wannan abu ne da aka yi da kyakyawar munufa, domin a hana fasa ƙauri da kuma hana shigo da wasu miyagun abubuwa ta ɓarauniyar hanya. To wannan abu ne mai kyau komai za a yi a yi a bi ƙa’ida.

Ba wata matsala in an hana shigo da ita za mu iya nomawa har ma mu ba wa ƙasashen duniya tunda muna da ƙasar noma ba laifi ba ne kuɗin da ake kashe wa wajen shigo da ita a ba wa manoman ƙasar nan su noma ta hanya mai inganci, domin in ka kula mu ƙasar nan ai muna da abinci kala-kala da Allah ya albarkace mu da shi. Ka sani ko a baya shinkafa ai ba abincinmu ba ne, shinkafa a da ta masu kuɗi ne kuma ba a cin shinkafa ko tuwon shinkafa ko a da sai gidan masu kuɗi ko kuma ga sallah. Saboda haka idan an yi haka daidai ne saboda za mu iya noma ta da kanmu. Wannan ni ina ganin ba wata matsala, domin wannan matakin ya sa an noma shinkafa da kayan amfanin gona mai yawa a ƙasar nan kuma yanzu Nijeriya ce take ciyar da ƙasashen Afirka da sauransu kamar yadda na gani a Burkina Faso in ka je Dawanau za ka ga yadda kasuwar take cika da kayan amfanin gona. Kawai dai mu dai matsalar babu wani tsari da zai taimaki ƙasar.

Yayin da ake ƙoƙarin hana shigo da shinkafa ƙasar na kuma a an yi shelar fitar da Doya ƙasar waje kuma  meye raayinka?

To ni a gani na ba wani laifi a fitar da doya ɗin domin ko ba komai shi chief Abdu obeye ya taimaki ’yan’uwansa Tibi su bunƙasa  noman Doya daidai.

To a ƙarshe wanne kira kake da shi ga al’umma?

To ni gaskiya kamar yadda na gaya ma, komai nawa a harkar noma na tashi, karatu ma da na yi Digiri a wata jami’a a Alabama da ke ƙasar Amurka akan harkar noma na yi, kuma noma akwai farin ciki a cikinsa, akwai kuma sa lafiya a gare shi, domin ka ga yanzu da na je gona yau na yi gumi sosai to ka ga wannan ƙarin lafiya ne kuma in kana da abincin kanka, kuma harkar noma ita ce mafita daga maula da tumasanci da dai sauran duk wani abin ƙi. Kuma ina so mutane su guji dogaro ko neman muƙamin gwamnati don a huta a rungumi noma.

 

Exit mobile version