Noman auduga a kasar nan, musamman a Arewacin Nijeriya na da cikakken tarihi, a yankin idan yik la’akari da irin gudunmawar da fannin ya samar wajen bunkasa tattalin arzikin a yankin tun kafin Nijeriya ta samu ‘yancin kanta daga gun turawan mulkin mallaka.
Har ila yau, tarihi ya nuna cewa, noman na Audugar a kasar nan, bayan samun ‘yancin kan Na kasar, fannin ya taimaka matuka wajen habaka tattalin arzikin kasar baki daya.
- Da Dumi-Dumi: Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta Rasu
- Da Dumi-dumi: Shugaban Kwamitin Amintattu Na PDP Yayi Murabus
Sai dai, wani abin takaici shine, wasu masana a noman na Audugar a kasar nan, sun daidaitu a kan cewa, har yanzu da akwai alamun da ke nuna cewa, fannin na noman audugar a kasar nan, na fuskantar wasu manyan kalubalen da ke ci gaba da janyo wa fannin koma baya.
A bisa hasashen da masanan suka yi, har yanzu ba a samu canjin da zai sa kasar nan ta shiga cikin sahun kasashen duniya da suka yi fice a harkar noman Auduga ba, musamman idan aka yi dubi da yadda samar da ingantaccen Irin noman Audugar a kasar ya janyo fannin a ‘yan shekarun baya, ke fuskantar barazana.
A cewar masanan, wannan halin ya sa ana barin Audugar da aka noma a kasar aka kuma kai ketare don sayar wa, ba ta cika samun karbuwar da ake bukata ba a kasuwar ta duniya.
Sai dai, idan aka yi la’akari da yadda wasu cibiyiyin da ke gudanar da bincike a bangaren samar da ingantaccen irin noman na Audugar a kasar nan suka yunkuro, za a iya cewa, a yanzu Nijeriya ta dora dambar bunkasa nomanta, musamman domin ta samu karbuwa a kasuwar ta duniya.
Masanan sun sanar da cewa, a shekarun baya ana tantance ingantacciyar audugar wanda hakan ya taimaka wa, fannin Da kima manoman na audugar a kasar nan, musamman domin ta yi Daraja a kasuwar duniya Sai dai, masanan sun bayyana cewa, a bisa yunkurin da cibiyoyin gudanar da da bincike suka yi don tantance ingantaccen Irin na Audugar a kasar nan, zai taimaka wajen kara farfado da nomanta a kasar, inda hakan zai taimaka don Audugar da ake noma wa a kara ta yi Kunnen Doki da sauran wacce sauran kasashen duniya ke kai wa kasuwar ta duniya domin sayarwa.
A cewar su, akwai kuma bukatar gwamnatin tarayya ta zuba kudade masu yawa domin cibiyoyin su kara zage wajen gudanar da bincike don a samar da ingantaccen Irin na Audugar a kasar nan.
Misali, don a tabbatar da an samar da ingantaccen irin na audugar, a kwanan baya ne Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello, ta kuduri aniyar samar da ingantaccen Irin na Audugar wanda kuma cibiyar ta ce, hakan zai taimaka matuka wajen kara farfado da nomanta a kasar nan.
Cibiyar za ta yi nazarin ingancin irin da noman da kasuwancinta da matsaloli da Masanan sun yi nuni da cewa, rashin samar da ingantaccen tsari a fannin na noman audugar a kasar nan, na daya daga cikin matsalolin da fannin a kasar nan ke fuskanta.