Connect with us

KASUWANCI

Noman ‘Cocoa’ Yana Kwan Gaba Kwan Baya A Nijeriya

Published

on

Gidan Cocoa dake garin Ibadan, an gina shi ne ribar da aka samu ta sayar da Cocoa a kasashen  waje ginin mai tsawon hawa ashirin da shidashi ne wanda yafi ko wanne gini tsawo a kasar nan.

Ribar da aka samu a sayar da shi an mashi babban farashi a matsayin amfanin gona mai mahimmanci da ake sarrafa alewa kuma anyi amfanidashi wajen hakaba ikimin zamani da kiwon lafiya da samar da ci gaba

musamman a karkara da gudanar da sauran ayyuka.

Sai dai abin takaici labaran na gidan Cocoa a yau ya canza, inda gidan ya  koma tamkar fako, fentin gidan kanshi duk ya koke rufin sa ya rubza ofishin kuma babu komai a ciki.

A cewar Pa Olusina Adebiyi, gidan a baya abin tinkaho ne  yankin yamma, inda ya yi nuni da tsohuwar yankin yamma wadda aka sake mata fasalizuwa jihohin da aka ware a shekarar 1967.

Pa Olusina Adebiyi, tsohon ma’aikaci a gidan kuma dan shekara tamanin da biyar a hirar sa da kafar dillancin labarai ta AFP yaci gaba da cewa, “a yanzu idan kaje gidan komai ya lalace.

Aikin noma a shekaru da dama da suka shige shi ne abinda Nijeriya take tinkaho dashi wajen tattalin arzikin kasar, inda kuma yake samar daayyukan yi ga sama da alumma saba’in tun kafin a gano mai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnatin sa, a yanzu suna yin iyakar kokari wajen farfado da aikin noma don kauracewa yin dogaro

akan mai kachokam.

Daya daga cikin fannin da ake ganin ya kai wani matsayi samar da ci gaba shi ne na ci gaban noman Cocoa, musamman ganin yadda kungiyar tanoman Cocoa ta kasa (CAN) ta tsara shiri na tsawon shekara goma don

inganta noman Cocoa a Nijeriya.

Shugaban kungiyar Sayina Riman ya ce,

“mun dauki shawarwari da zasu samarwa da fannin noman Cocoa alkibla a kasar nan.”

A cewar sa, “muna kuma fatan wadannan shawarwarin za’a wanzar dasu a bisa adalci don amfanin fannin.”

Riman ya yi nuni da cewa, farashin ya ban-banta, inda ya kara da cewa ta hanyar cocoa gwamnati a baya tana samun kusan kashi saba’in nakudin shiga ga gwamnati da kuma samar da kudin shiga kashi chasa’in na kudin shigar kasar waje wanda a baya dasu ne aka yi amfani wajen samar da mai a kasar nan.

Ganin yadda mai ya tashi sai farashin cocoa ya sauka a shekarar 1970.

A cewar wasu bayanai da suka fito daga sashen abinci da da aikin noma na majalisar dinkin duniya, sana’ar Cocoa babbar sana’ace da aka yi watsi da ita a nahiyar Afrika, inda sarrafa shi a shekarar 2016 ake samun tan 237,000. Kasar Ibory Coast tana samar da tan miliyan 1.47

inda kasar Ghana kuma take samar da tan  miliyan 859,000.

Nijeriya tana yin noman cocoa sau biyu daga watan Afirilu zuwa watan Yuni da kuma wanda ake shukawa daga cikin watan watan Okutoba watan

Disamba.

Oluranti Adeboye a cikin gonar sa ta noman Cocoa mai ika uku a cikin kauyen Sofolu a cikin jihar Ogun, yana ta fama da gudanar da aiki a mgonar sa da adda da kuma doguwar sanda.

A cewar sa, yayin a wannan shekarar yana da kyau sosai, ruwan damina na farko yana taimakwa yabanya.

Manomin siriri dan shekara 62 kuma ma’aikacin gwamnati ya yi shiri tsaf don tsikar cocoa sa da ya nuna.

Ya bayyana cewar, wannan cocoa da ya samu na bana yafi na wanda ya samu a  shekarar baya.

Yana a tube yana tsikar cocoan yana sanyawa a cikin buhu kafin ya shanya shi a cikin don fitar dashi a kai  kasar waje sayarwa.

Adeboye ya sanar da cewar, manoma suna tabka asara saboda cututtukan da suka aukawa cocoan da kuma karancin iri da ake fama dashi.

Bishiyoyin an shuka sune sama da shekar goma.

Shima wani manomin mai suna Sunday Ojo Folorunso, daga makwabtan jihar Ondo, ya koka ne akan farashin na cocoan, inda ya ce, a yanzu haka ana sayar dashi akan naira 650 zuwa naira 680.

Manona a kasa Ibory Coast da Ghana an inganta sana’ar su ta noman.

A cewar ciuyar noma ta (IITA dake Ibadan an taimakawa manoma kimanin ika 3000 bisa dari zuwa ika 800, inda hakan yake samar masu da kudi nshiga da inganta noma su.

 

 
Advertisement

labarai