Noman Shinkafa A Nijeriya: Ina Ribar Ta Ke?

Tare da Bichia Maisango

Tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce “Jiki magayi”. Domin kuwa wahalar da masassarar tattalin arziki ya jefa ‘yan Nijeriya a ciki, ya haifar da wani yunkuri na neman mafita da ‘yan kasa suka yi. Bugu da kari, tsadar abubuwan masarufi, ya zo da ‘yar manuniya cewa, ba za a fita daga wannan azabtaccen yanayi ba, idan har ‘yan kasa ba su yunkura ba wajen samar da abinci a cikin gida, domin kashe gwiwar shigo da na waje.

Bincike a daya hannun kuma ya nuna cewa, shinkafa ita ce abincin da ‘yan Nijeriya su ka fi shigowa da ita, daga kasashen ketare, kamar yadda alkaluma suka nuna cewa, ana cin shinkafa a Nijeriya akalla kimanin tan miliyan 6.5, a shekara daya kacal, wadda kuma fiye da rabin wannan adadi ana shigo da shine daga kasashen ketare, musamman kasar Tailan. Daga nan ne masana suka kididdige cewa, ‘yan Nijeriya su na kashe kimanin Dalar Amurka bilyan 2 wajen sayen shinkafar ketare.

Ta haka ne gwamnati a nata bangaren ta bijiro da wasu tsare-tsare da manufofi da za su tabbatar an karfafa gwiwar manoma shinkafa, domin cin ma muradan samar da yalwataccen adadi da zai ishi bukatun ‘yan kasa, a cikin wasu shekaru kalilan masu zuwa.

Hakika an ga wasu canje-canje na cigaba ta yadda manoma suka tunkari noman shinkafa a shekarar da ta gabata, kama daga Arewacin kasar nan zuwa Kudanci. Amma wani hanzari ba gudu ba, shi ne yadda har yau masu ruwa da tsaki suke barin baya da kura, ta wajen mai da hankali ga amfani da tsofaffin dabarun noma, wanda hakan ba karamin tarnaki ya ke kawowa ba, wajen samun damar cimma muradan da aka sa a gaba cikin kayyadajjen lokaci.

A jihohin da na kai ziyazar gani da ido, na samu damar ganawa da manoman shinkafa, yayin da na kai kewaya wasu manyan gonaki a jihar Kebbi da jihar da na fito, ta Kano, na nazarci yadda manoman ke amfani da tsofaffin dabarun noma kama daga sharar gona, yafe, dashe, saka taki, nome ciyawa har zuwa girbi. Ba anan abin ya tsaya ba, ganin yadda ake amfani da matasa majiya karfi wurin bugun shinkafa ba ji, ba gani da manyan sanduna domin sussuke ta, kafin a zo ga casa, wanda itama ake yi da injina samfurin tahuna, wadanda ba su iya rabe shinkafa da tsakuwa.

Gabadaya wadannan hanyoyin noman shinkafa sun dade da zama tsohon yayi a kasashen da suka yi fice a noman shinkafa a duniya.

Ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki a noman shinkafa su farga cewa, amfani da manyan injinan noma na zamani ne kadai zai iya tabbatar da cimma muradan da muka sa a gaba. Dole ne Kuma a ajiye amfani da kananan injinan casar shinkafa masu samfurin tahuna zuwa samar da manyan kamfanonin casa da sarrafa shinkafa zuwa ga matakin duddura ta a buhu, wanda zai yi daidai da irin na zamani, wanda ba su barin ko tsakuwa daya a cikin shinkafa.

Allah ya albarkaci Nijeriya musamman Arewaci da kasa mai yalwar noma wacce hakan dama ce, da bama iya amfanuwa da ita matukar sakamakon mayar da hankali da muka yi wajen ci-da-karfi a harkar noma.

Kasar Isra’ila ta zama abin koyi ga kasashen duniya da dama ta fannin noma, kasancewarta kasa mara fadin murabba’I, amma hakan bai hana ta cimma nasarar samar da kaso casa’in da biyar 95% bisa dari 100% na abincin da ‘yan kasar ke da bukata ba. Bama wannan kadai ba, kimanin kaso tamanin 80% bisa dari 100% na murabba’in kasar Isra’ila sahara ce ta mamaye ta, hadi da rashin isasshen ruwan sama, amma wannan bai hana masu ruwa da tsaki a fannin noma na kasar Isra’ila su yi nazari ba, don kirkiro hanyoyin da suka dace na samar da ingantaccen yanayin noma a kasar, wacce ta hada da jawo ruwa daga tekun maliya dake makwabtaka da kasar domin amfani da shi wajen noman rani a yankunan da sahara ta mamaye a kasar, tare da samar da iri na zamani da zai dace da yanayin kasarsu ta noma.

Haka zalika kasar Tailan, wacce ke shigo mana da mafi yawan shinkafar da mu ke amfani da ita na tsawon shekaru, ta kasance mai mayar da hankali akan dabarun noma da fasahar zamani ta samar. Kasar Tailan ta kasance mai cike da tsuburai da tsandauri, amma hakan sai ya zamar musu izna wajen fadada bincike da gano dabarun da suka dace da yanayin kasarsu ta noma, wacce hakan ce ta kai su ga cimma muradunsu na noma.

Kira na anan ga manoma, musamman na shinkafa da kuma gwamnatin tarayya zuwa gwamnatotin jihohi shi ne, dole a sami sauyi wajen watsi da noman ci-da-karfi zuwa rungumar sabuwar fasahar noma ta zamani.

Tuni sabuwar fasahar noma ta zamani ta samar da injinan shuka,  injinan dashe, injinan zuba taki, injinan nome ciyawa da kuma manyan injinan feshin maganin kwari har zuwa uwa-uba injinan girbi da na sarrafa shinkafa da buhunce ta cikin sauki. Duk wannan manyan mashina su na aiki mai yawa cikin kankanin lokaci da sauki bayan taimakawa da suke matuka wajen ninka yawan amfanin gona, da hana asararsa.

Shima babban bankin manoma yana da muhimmiyar rawar takawa wajen shigo da manyan injinan aikin noman shinkafa domin kananan manoma su samu damar hada gwiwa tare da amfanuwa daga kwadagon wannan kayan aiki a cikin farashi mai rahusa. Shi ma adashin gata ga manoma yana da bukatar ingantawa.

A karshe dole mu yi kira ga cibiyoyin bincike akan harkar noman shinkafa, wanda ba za a barsu a baya ba, wajen tashi tsaye da bincike tukuru domin cigaba da sabunta irin shinkafa a zamanance mai afki. Ya zama wajibi ga wadannan cibiyoyi da su mayar da hankali wajen wayar da kan manoma shinkafa zuwa ga rungumar sababbin dabarun noma na zamani hannu biyu.

Exit mobile version