Manajin Darakta na Hukumar Tashar Jirgin Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bukaci da a yi nazari kan wanzar da tsarin tashoshin Jiragen Ruwa kasa da kasa da samar da kayan tabbatar da tsaro ISPS, musamman domin a kara samarwa da fannin tsaron da ya kamata.
Abubakar ya yi wannan kiran ne, a jawabinsa a taron kasa na 2024 da kungiyar jami’an ma’aikata a Tashoshin Jirage Ruwa ta kasa wato SOFN.
- Harajin “VAT” Zai Kara Wa Al’ummar Kasar Nan Kuncin Rayuwa Ne Kawai – Gambo Danpass
- An Jinjina Wa Tawagar NPA Kan Samun Nasarar Sayar Da Danyen Mai Da Takardar Naira
Ya yi nuni da cewa, yin nazarin zai tabbatar da samar da wadataccen tsaro, musamman ta hanyar samar da kayan zamani na wanzar da tsaro, a daukacin tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
“A yayin da muke yin dubi da shekarun baya, ya kamata mu san gudunmawar da samar da tsaro ke bayawa a tekunan kasar nan, musamman domin a samu damar gudanar da hada-hadar kasuwanci na kasa da kasa tare da kuma tabbatar da, ana samar da kariya ga direbon Jiragen ruwa da kuma ma’aikatan da ke aiki a tashoshin Jiragen ruwa, “ inji shi.
Ya sanar da tsarin na ISPS Code wanda ya fara aiki gadan-gadan 2004, zai taimaka wajen kara samar da tsaro a tashoshin Jiragen ruwan kasar da kuma dakile dukkan wata barazana ta rashin tsaro a fannin.
A cewarsa, “Ga Nijeriya, tamkar kira ne na fara zuba hannun jari domin a kara habaka tsarin, wanda bai kawai bayar da kariya ga tashoshin Jiragen ruwan kasar ba, amma a kara kare martabar kasar mu, wacce take ita ce, uwa maba da mama, ga sauran kasashen da ke a cikin Afirka.
Ya sanar da cewa, shirye-shiyen wanzar da tsarin na ISPS Code 2020 a duniya, ya fuskance kalubale wanda suka hada da; ayyukan ta’addanci, ‘yan fashin teku, safarar haramtattun kaya da sauransu
Sai dai, Dantsoho ya sanar da cewa, yanu duniya na sauya wa ne, wanda hakan ya sanya hukumar ta NPA, ta gay a kamata ta rungumi tsarin na ISPS Code, tare da kuma wanzar dashi, gadan-gadan.
Dantsoho ya ci gaba da cewa, a namu bangaren a hukumar, muna bukatar sama da sauyi, wanda hakan ya sanya muka sabunta kayan aiki, musamman samar da kayan aiki na kimiyyar zamani, ana kuma kara samun masu zuba hannun jari da horar da jami’an tsaron mu, domin dakile dauk wata barazana da za ta iya kunno kai.
Ya sanar da cewa, hukumar tare da hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jihohi, masu kula da kayan aiki a tashoshin Jiragen ruwan kasar da kuma aboan hadakar mu na kasa da kasa, suna gudanar da aiki, kafada da kafada domin kara tabbatar da tsaro a fannin.