Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta sha alwashin gudanar da sahihin kidayar mutane da gidaje a fadin Nijeriya a 2023.
Kwamishinan hukumar NPC a Jihar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai dangane da bude shafin yanar gizo na daukar ma’aikatan da za su gudanar da aikin kidayar.
Ya yi nuni da cewa bin hanyar zamani wajen daukar ma’aikatan kidayar wani bangare ne na kudurin hukumar na gudanar da sahihi kuma ingantacciyar kidaya.
Injiniya Almu ya kara da cewa yawan ma’aikatan kidayar da za a dauka ya danganta da yawan yankuna da ke fadin kasar nan.
Ya ce hukumar ta kafa tawagar daukar ma’aikatan kidayar na kananan hukumomi da na jiha domin tabbatar da ganin an dauko mutanen da ke yankunan don gudanar da aikin.
Kwamishinan hukumar ya ce ma’aikatan da ake bukatar dauka sun hada da masu bayanai, jami’an bayar da horo, masu duba aiki, masu daukar bayanai da dai sauransu.
Ya bayyana cewa daga cikin ka’idojin yin rijistar ma’aikatan akwai lambar NIN da ta asusun ajiya na banki.
Ya kara da cewa shafin daukar ma’aikatan kidayar zai ci gaba da zama a bude har zuwa watan Disamba, amma za a rufe shi na wani lokaci tsakanin ranakun 7 zuwa 13 ga wannan watan na Nuwamba.
Kwamishinan ya shawarci masu neman aikin su yi taka tsan-tsan don kar su tura bayanai ba daidai ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp