• English
  • Business News
Saturday, September 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NWC Ne Kadai Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje Daga Shugabancin APC – Abdulkarim Kana

by Sadiq
1 year ago
in Labarai
0
Ganduje Ya Zargi ‘Yan Siyasa Da Hannu A Haddasa Rikice-rikicen Zabe
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Abdulkarim Kana, ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa (NWC) ne, kadai ke da alhakin dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Kana, ya bayyana haka ne yayin hira a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

  • Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki 
  • Matashiya Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Shan Maganin Ƙwari A Delta

Ya yi wannan martani ne kan dakatarwar da wasu shugabannin jami’yyar APC a mazaɓar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, suka yi wa shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Shugabannin jam’iyyar a mazaɓar sun dakatar da Ganduje, bisa zargin cin hanci da rashawa, a lokacin da yake gwamnan Kano.

Sai dai shugabancin jam’iyyar APC na Jihar Kano, ya soke dakatarwar tare da korar waɗanda suka dakatar shi daga jam’iyyar.

Labarai Masu Nasaba

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano, ta jaddada hukuncin dakatarwar da aka yi wa Ganduje na wucin gadi, zuwa lokacin da za ta kammala shari’a kan zarge-zargen da ake masa.

Alkalin babbar kotun da ke Kano, wanda tun farko ya tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje, ya janye dakatarwar da kotun ta yi wa tsohon gwamnan na Kano a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Da yake magana a ranar Litinin, Kana ya ce babu wata ƙungiya a jam’iyyar da ke da hurumin dakatar da kowane ɗan jam’iyyar face kwamitin ayyuka na jami’yyar na ƙasa.

A cewarsa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar, dole ne a bi wasu matakai kafin zartar da irin wancan hukunci da aka ɗauka a kan Ganduje.

“Duk waɗannan hanyoyi dole ne a kare su kafin zartar da irin wannan hukunci idan an kammala bincike, babu wata ƙungiya a APC da ke da hurumin dakatar da duk wani ɗan jam’iyya da ake bincike a kansa sai kwamitin ayyuka na ƙasa,” in ji shi.

Kana, ya ce waɗanda suka dakatar da Ganduje babu wanda ya san da zamansu a jam’iyyar.

Ya ce: “…Na san wasu ɗaiɗaikun mutane, su ba shugabannin mazaɓar Ganduje ba ne, kuma ba shugabannin unguwanni ba ne. Tun da farko, lokacin da waɗannan bayanai suka bayyana a gare mu, abu na farko da muka yi shi ne bincike kuma muna da hanyar da za mu tabbatar da ko akwai waɗancan zarge-zarge.

“Wannan babban zargi ne, cewa wata ƙungiya a jam’iyyar za ta ɗauki wannan mataki. Mun gudanar da bincikenmu, kuma ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba muka gano waɗanda suka ce sun dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, ba ‘ya’yan jami’yyar ba ne a mazaɓar Ganduje ba.

“Ofishina bai tsaya karɓar rahotanni daga ɗaiɗaikun mutane dangane da sahihancin wannan zargi ba, mun gayyaci kwamitin ayyuka na jiha tare da na mazaɓa zuwa Abuja domin tattaunawa da su, kuma na dage sai sun zo da katin shaida da kuma katin zaɓensu.

“Lokacin da suka zo da katin shaidarsu, sai muka gano cewa waɗanda suka bayyana a talabijin kan wancan zarge-zarge ba su ne a jikin katin shaidar ba, wannan lamari yana da girman gaske.

“Hakan ne ya sanya ba mu ɓata lokaci ba wajen sanya jami’an tsaro cikin lamarin domin gudanar da bincike kan dalilin da ya sa waɗannan mutane za su yi wannan zarge-zarge, ‘yan damfara ne, abin da suke yi kenan. Kuma mun karɓi koke daga shugabannin mazaɓar na gaskiya wanda muka aike wa ‘yan sanda, yanzu maganar tana gaban ‘yan sanda domin gudanar da bincike.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCCin Hanci Da RashawaGandujekanoNWCShugabancin APCZargi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki 

Next Post

Sabon Harajin Tsaron Yanar Gizo Bai Shafi Hada-hadar Kudi 16 Ba – CBN

Related

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai
Labarai

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

49 seconds ago
Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro
Tsaro

Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro

41 minutes ago
Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi

1 hour ago
An Shirya Haɗin Gwiwa Da Hukumomi Don Magance Matsalar Ambaliyar Ruwa
Manyan Labarai

An Shirya Haɗin Gwiwa Da Hukumomi Don Magance Matsalar Ambaliyar Ruwa

2 hours ago
Majalisar Tarayya Ta Magantu Kan Gawar Da Aka Samu A Harabarta
Manyan Labarai

Majalisar Tarayya Ta Magantu Kan Gawar Da Aka Samu A Harabarta

3 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki

4 hours ago
Next Post
Sabon Harajin Tsaron Yanar Gizo Bai Shafi Hada-hadar Kudi 16 Ba – CBN

Sabon Harajin Tsaron Yanar Gizo Bai Shafi Hada-hadar Kudi 16 Ba - CBN

LABARAI MASU NASABA

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

September 13, 2025
Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro

Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro

September 13, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi

Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi

September 13, 2025
An Shirya Haɗin Gwiwa Da Hukumomi Don Magance Matsalar Ambaliyar Ruwa

An Shirya Haɗin Gwiwa Da Hukumomi Don Magance Matsalar Ambaliyar Ruwa

September 13, 2025
Majalisar Tarayya Ta Magantu Kan Gawar Da Aka Samu A Harabarta

Majalisar Tarayya Ta Magantu Kan Gawar Da Aka Samu A Harabarta

September 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki

September 13, 2025
PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya

PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya

September 13, 2025
Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

September 13, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

September 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Inganta Muhimman Abubuwan More Rayuwa Don Ci Gaban Ƙasa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Inganta Muhimman Abubuwan More Rayuwa Don Ci Gaban Ƙasa

September 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.