Oba Na Benin Ya Koka Dangane Da Matsalar Tsaro A Nijeriya

Oba na Benin mai girma Ewuare II, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a fadin kasarnan. Oba na Benin ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a garin Benin a lokacin da ya karbi bakuncin Mejo Janar Anthony Omozele wanda shi ne GOC 2 Division na rundunar sojin Nijeriya a yayin da suka kai masa ziyara a fadarsa.

Har wala yau Oba na Benin ya nuna damuwarsa dangane da ayyukan ‘yan bindiga da masu tada kayar baya a wadansu sassan Nijeriya, inda ya yi kira ga ‘yan kasa da su dage da addu’a domin magance kalubalen da ke fuskantar kasarnan.

Oba na Benin ya nusasshe da sojojin cewa an kafa su ne domin su kare kasarnan daga hare-haren makiya na waje, ya ce; abin takaici ne a ce sojojin yanzu sun koma magance tsaron cikin gida.

Ya shawarci shugabannin Nijeriya da su rika sauraren koke-koke da kiraye-kirayen al’umma domin ganin an bunkasa hanyoyin magance matsalolin kasarnan. Sannan Oba na Benin ya mika ta’aziyyarsa ga rundunar sojin bisa rasa rayukan sojoji da take yi musamman a arewa maso gabashin kasarnan.

 

Exit mobile version