Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ƙaryata raɗe-raɗin da ke cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, ya yi amfani da kuɗin jihar wajen tallafa wa kamfen ɗinsu na neman shugabancin ƙasa ba.
Akwai raɗe-raɗin da ke cewa Okowa, wanda ya kasance abokin takarar Atiku, ya karkatar da kuɗaɗen jihar Delta don tallafa wa takarar PDP a 2023. Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Abdul Rasheeth, ya bayyana cewa ya ɗauki nauyin kamfen ɗinsa ba tare da dogaro da abokan takararsa ba.
- 2027: Da Yiwuwar Atiku, Obi, Kwankwaso Su Yi Kawancen Siyasa – PDP
- Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Kudirin Kara Yawan Membobi Daga 360 Zuwa 366
Rasheeth ya bayyana cewa zaɓin abokan takarar Atiku, kamar Ben Obi a 2007, da Peter Obi a 2019, da Okowa a 2023, ya ta’allaka ne kan cancanta ba tare da la’akari da goyon baya na kudi ba.
Ya ce waɗannan zarge-zargen ƙarya ne kuma suna fitowa ne daga mutanen da ke da wata manufa ta kashin kansu kan Okowa.