Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

‘Okay’ Din Ciyaman, Sam Nda-Isaiah (3)

by Daurawa Daurawa
December 28, 2020
in MAKALAR YAU
4 min read
Shigo-shigo Ba Zurfi, Tinubu!
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ci gaba daga makon da ya gabata…

Stanley ne ya fada min cewa ai idan ka tura wa Ciyaman aiki ya turo maka da sakon ‘Okay’ yana nufin an baka izinin ka ci gaba kenan. Ya dan kara min da wasu shawarwari game da wanne irin mutum ne Ciyaman, kuma ya ake zama da shi. Daga cikin abin da na rike sosai akwai batun cewa, Ciyaman na so ka rika takura mishi idan ya sa ka aiki; wanda a hankali na fahimci wannan.

samndaads

Gabadaya labarin fushi da hayaniyar Ciyaman na ke ji a wurin wasu kafin wata ranar Talata, bayan mun yi kamar watanni hudu da fara aiki. Sai masu aikin kwamfuta suka hade kai suka ce ba za su yi aikin Jaridar Laraba ba, har sai an biya su albashinsu na wata biyu. Duk da na san da shirinsu, ni dai ban yi kasa a gwiwa wurin ci gaba da hada aiki ba, har zuwa yamma. Sannan ne na sanar da Stanley cewa, zan kira Ciyaman na sanar da shi halin da a ke ciki, domin kuwa idan har na yi shiru jaridar washegari ba ta fito ba, zan kasance cikin manyan masu laifi.

Hankalina a tashe na sake kiran Stanley, na sanar da shi yadda muka yi da Ciyaman. Nan da nan ya garzayo ofis. A haka aka yi ta maida magana tsakanin manyan ma’aikatan kamfanin. Wasu daga cikinsu sun yi ta ganin laifina akan bai kamata na sanar da Ciyaman halin da a ke ciki ba, domin su ya yi wa dirar mikiya. Amsa daya na yi ta ba su, “Idan jarida ba ta fito ba, ni ne Edita, kaina za ta kare.”

Tun farkon fara aikin, a duk lokacin da muka hadu da Ciyaman yabonmu ya ke yi. Wasu lokutan ma sai na dan ji kunya, yadda ya ke caccakar sauran ma’aikatan sashen turanci. Ya rika cewa, Yara sun zo sun fi ku sanin kan aiki. Wannan yabo da jinjinawa ta Ciyaman ta ja mana tsangwamar da ba iya bayyanata a fili, sai dai a bizne ta a zuciya.

Lokacin da aka zo maganar tafiya aikin Hajji na shekarar 2018 aka sanar da ni cewa ni ne zan tafi. Tabbas na ji dadin shaida biyu da aka bayar. Ta farko, Babban Manajin Daraktan LEADERSHIP, Abdul Gombe ya tambayi Shugabar sashen kudi shin idan ana so a karrama wani a sashen Hausa, wa ta ke ganin ya kamata. Sai ta kira sunana. G.M.D ya tambayeta ko mene ne dalili. Sai ta ce: “Bai taba cewa BA ZAI YIWU BA. Idan ka tambaye shi yaushe za a kawo aikin kudi, zai ce kudi sun kusa zuwa. Kuma yana kawowa din.”

Shaida ta biyu ita ce ta Ciyaman. Ko da na kira don sanar da shi cewa zan tafi Hajji. Idan kuma bana nan, Mataimakina na lokacin (Editan Jaridar LAHADI a yanzu), Malam Bello Hamza zai rike aikin har na dawo. Cikin harshen Ingilishi Ciyaman ya ce, “Ai na fada maka, gobenka tana da haske. Kuma za ka yi nisa a wannan harkar. Ka ci gaba da dagewa.”

Allah Sarki! Akwai watarana da na tafi Kano zance, lokacin ban yi aure ba. Na isa Kano ranar Juma’a, ina gidan su Matata da yamma sai ga kira daga Ciyaman yana tambayata ko ina gari. Na ce, mishi a’a, har da ‘yar guntuwar karya, na ce ina Kaduna alhali ina Kano. Sai kuwa ya ce, na zo yana nema na. Na ce, toh. Har ga Allah na yi niyyar na bari sai Lahadi sannan zan je na same shi. Ranar Asabar da safe sai ga kira daga Geoffrey (mutumin da ban taba ganin mai ji-ji da kai irinsa a LEADERSHIP ba), ya bukaci na tura masa adireshin I-mel dina. Ban ma tsaya tambayarsa dalili ba, na tura.

Bayan La’asar sai ga sakon I-mel daga Geoffrey, wai umurni daga Ciyaman, na zama Editan Jaridar LEADERSHIP ta turanci. Ina gani na kira Geoffrey a waya, na ce mishi ba zan yi ba. Nan fa ya harzuka, ya fara fada, yana cewa ai sai na kira Ciyaman na sanar da shi, “Kuma ka kwana da sanin babu wanda ya isa ya ki amsar umurnin Ciyaman.” Na katse shi mishi hanzari, na sake cewa, ba zan yi ba, zan kira Ciyaman din.

Na kira Ciyaman, yana dauka ya ce, me ya sa har yanzu ban zo ba. Na ce, zan zo, amma wannan takardar mukamin da aka buga bana jin zan yi. Sai ya ce, “don me? Ka zo ina jiranka. Karfe hudu na yamma na dauki Rabi’u Ali Indabawa muka bar Kano zuwa Abuja. Sai bayan Magriba muka bar Kaduna, ga shi ana ruwan sama, cikin zulumi haka muka yi ta nausawa a hankali. Ba mu shiga gidan Ciyaman ba sai karfe 11:30 na dare. A nan na kwakkwafe Ciyaman, har ya gamsu. Washegari sai ga sabuwar takarda, an fasa sabon mukamin da aka yi min. Wannan lamarin ya ba manyan ma’aikatan LEADERSHIP mamaki, tun lokacin suke kirana da ‘Mutumin Ciyaman’.

Tabbas! Mun yi zaman arziki da rabuwar arziki da Ciyaman. Duk zafin ransa da saurin fushi, bai taba zagina ba kamar yadda ya ke zazzage ma’aikatansa. Idan na ce ina son yin magana da wani Gwamna, Minista ko babban mutum, lamba yake aiko min. Sannan ya kan ce, idan na kira ba a dauka ba, na sanar da shi, zai yi min iso. Mako biyu kafin ya rasu ya bani wani aiki da nake ba shi rahoto kullum ta ‘Whatsapp’, hatta ranar Juma’ar da ya rasu sai da na tura. Sakon da bai bude ba kenan, ballantana mu tattauna.

SendShareTweetShare
Previous Post

Darajar Naira Zai Sake Zabgewa A 2021 – CBN

Next Post

Sam Nda-Isaiah (1962-2020): Yau Ake Binne Gawar Shugaban LEADERSHIP

RelatedPosts

Kan Iyakokin Najeriya

Baya Ba Zani: Wadanne Dalilai Suka Sa Aka Bude Kan Iyakokin Najeriya?

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Gwamnatin Najeriya mai abin mamaki, wani lokaci idan ta yi...

Barna

Taimako Ko Barna? 24

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Idan ka gabatar da wannan maudu’in a matsayin tattaunawa a...

APC

Canjin APC Ko Canjin Rigar Mahaukata?

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Abubuwa sun bi sun damalmale, komai ya rincabe, kayan masarufi...

Next Post
Shugaban Leadership

Sam Nda-Isaiah (1962-2020): Yau Ake Binne Gawar Shugaban LEADERSHIP

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version