Gabanin shiga zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a Jihar Kogi, mataimakin gwamnan jihar, Edward Onoja, da shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar, Mohammed Abdulkareem Asuku, sun janye daga neman takarar gwamnan jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da zaben fidda gwani na takarar gwamna a ranar Juma’a 14 ga watan Afrilu, 2023.
Matakin nasu na zuwa ne bayan wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da gwamnan jihar, Yahaya Bello ya shirya a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Lokoja, babban birnin jihar a ranar Alhamis, inda gwamnan ya bayyana dan takarar da yake so.
An tattaro cewa gwamna Bello ya zabi tsohon babban mai binciken kudi na jihar, Alhaji Ahmed Usman Ododo, a matsayin wanda zai gaje shi.
A halin da ake ciki, Onoja da Asuku sun sanar da janyewarsu daga takarar gwamnan a shafukansu na Facebook jim kadan bayan kammala taron.
Mataimakin gwamnan, Onoja, wanda mutane da yawa suka yi tunanin zai gaji Gwamna Bello a baya, ya wallafa wani sako a shafin Facebook, wanda ke cewa: “Allah ya kara daukaka ga rayuwa da lafiya. Ina godiya ga shugabana, Alhaji Yahaya Bello da dukkan magoya bayana saboda soyayya da addu’o’inku, hakuri da juriya, ina mai godiya har abada.”
A nasa bangaren, shugaban ma’aikatan gwamnan, Asuku, wanda kuma ake ganin yana kan gaba saboda kusancinsa da gwamnan, ya wallafa nasa jawabin kamar haka: “Alhamdulillah!
Dukkan yabo da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki mafi daukakar halittu baki daya kuma wanda ya kiyaye rayuwata da ta dangina da masoyana da su shaida wannan lokaci a rayuwata. Ina matukar godiya ga mai girma Gwamna, bisa dukkan abin da Allah Ya yi amfani da shi wajen aikatawa a rayuwata. Don haka nake mika kaina a bainar jama’a ga hukuncin da aka yanke a yau kuma zan ci gaba da kasancewa da aminci da sadaukar da kai ga jam’iyyata ta APC wajen samun nasara a zaben da za a yi a nan gaba.”
A wani lamari makamancin haka, sauran masu neman takara kamar Mista David Adebanji Jimoh; tsohon kwamishinan kudi, Asiwaju Ashiru Idris; Okala Yakubu, da Momoh Jubril su ma sun janye daga neman takarar gwamna.