Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC), ta zabtare adadin man da ta bai wa Nijeriya ta dinga fitarwa kowacce rana daga ganga miliyan daya da dubu 826 kowacce rana zuwa ganga miliyan guda da dubu 742.
Bayan wani taro da kungiyar ta gudanar domin daidaita farashin man wanda ya fadi kasa da Dala 90 a kasuwannin duniya a makon jiya, OPEC ta ce Nijeriya za ta dinga fitar da ganga miliyan guda da dubu 742 daga watan Disamba mai zuwa, yayin da aka ragewa Sudan nata zuwa ganga dubu 72.
- Mutum 30 Sun Nutse A Ruwa Yayin Tsere Wa Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Kotun Daukaka Kara Ta Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Su Yi Sulhu Da ASUU A Wajen Kotu
Wannan mataki na zuwa ne a dai-dai lokacin da Nijeriya ke fama da matsalolin cikin gida wajen samar da man da ake bukata, sakamakon yadda barayi ke fasa bututun man suna sace shi.
Sanar da daukar wannan mataki da OPEC ta yi ya sanya farashin man Nijeriya da ake kira ’Bonny Light’ ya tashi nan take zuwa Dala 93 da Centi 36 kowanne ganga, sabanin yadda kasar ta yi kasafin kudinta a kan Dala 62 na farashin man.
Gwamnatin Nijeriya ta ja kunnen hukumomin tsaron kasar na a kan yadda ake fama da matsalar satar man, wanda kamfanin NNPC ya ce yana asarar akalla ganga dubu 400 kowanne mako.