Shahararren dan wasan Nigeriya, Victor Osimhen ya zama dan wasa daga nahiyar Afirka na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar Seria A ta kasar Italiya.
Dan wasan, mai shekara 26 wanda ya ke buga kwallo a Napoli ya zura kwallaye 26 a kakar wasan da aka kammala.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 11, Sun Rusa Sansanoni A Dajin Sambisa
- Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Nada Masu Bashi Shawara 20
Osimhen ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Seria A a karon farko cikin shekaru 30 kuma yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraruwar su take haska wa a yanzu.
Har wa yau, dan wasan ya kasance gwarzon dan wasan Seria A a wannan kakar.
Tuni Manchester United da Chelsea da Real Madrid suka fara zawarcin dan wasan wanda ake ganin zai iya komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin nahiyar turai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp