Kwamitin Hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda (PCRC), ya zabi sabbin Shugabannin gudanarwa za su jagoranci kwamitin a jihar Adamawa.
Da yake jawabi a bikin rantsar da sabbin shugabannin a Yola, shugaban kwamitin na kasa, Mogaji Ibraheem Olaniyan, ya nemi shugabannin da su yi aiki tukuru ta yadda jihar za ta zama abin koyi ga sauran jihohi.
- CPPCC Ya Rufe Cikakken Taronsa Na Shekara-shekara
- Xi Ya Halarci Zama Na Biyu Na Taron Shekara Shekara Na Majalisar NPC
Olaniyan, ya ya kuma yi kira ga shugabannin da su bi dukkan hanyoyin da su ka dace wajan ganin kwamitin ya kai ga mataki na gaba.
A jawabinsa, shugaban kwamitin na yankin jihohin Arewa maso gabas, Attah Mustapha, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben ba tare da hamayya ba, inda ya ce, kwamitin zai taimaka wa aikin ‘yansanda wajen ganin ya yi tasiri da samun nasara a jihar.
A nasa jawabin, zababben shugaban kwamitin PCRC na jihar Adamawa, Musa Bubakari Kamale, ya yi alkawarin yi wa kowane mamban kwamitin adalci da samar da daidaito tare da rokon addu’o’i daga mambobin domin samun nasara