Idris Aliyu Daudawa" />

PDM Da PDP Sun Samu Umurnin Kotu Na Duba Kayan Zabe A Nasarawa

PIC.8. FIELD TEST OF INEC SMART CARD READER AT ONIGBONGBO IN LAGOS STATE ON FRIDAY (6/3/15). 1189/6/3/15/BOA/CVM/AIN/NAN

Kotun sauraren kararrakin zabe na gwamna da ke zaman ta a Lafiya jihar Nasarawa, ta ba Hukumar zabe mai zaman kanta umarni na su ba dan takarar gwamna na jam’iyyar PDM da kuma PDP, su samu damar duba kayayyakin zabe, wadanda aka yui amfani dasu ranar da aka yi zaben 9 ga watan Maris 2019 .
Musa Nagogo dantakarar gwamna na jam’iyyar PDM, ya shigar da karar ne inda ayake kalubalantar nasarar Injiniya A. Abdullahi Sule dantakarar jam’iyyar APC , saboda an manta da ba’a sa sunan shi ba da kuma alamar jam’iyya a takardar da aka yi zaben.
Shi kuma Dabid Ombugadu dan takarar jam’iyyar PDP shi yana kalubalantar zaben da aka yi ranar 9 ga watan Maris a jihar.
Dukkan su suna bukata ita Kotun ta tilkas ta ma Hukumar zabe mai zaman data basu dama ta su duba kayayyakin da aka amfani da su, kamar rajista da kuma wasu muhimman takardun da suke da , wadanda aka yi amfani da syu lokacin zabe.
Da yake yanke hukunci akan karar da su ‘yantakarar biyu suka shigar, shugaban ita kotun sauraren karar Abba Mohammed ya ba Hukumar zabe umarni na ta basu dama su duba kayayyakin da aka yi zabe.

Exit mobile version