Jam’iyyar PDP ta shaida wa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa ta kori shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu da kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa daga mukamansu.
Jam’iyyar PDP ta yi karar ne a kan zargin rashin bin doka da oda a tafiyar da al’amuran jam’iyyar na kasa da kuma ‘yan takararta.
- 2023: INEC Ta Samar Da Ingatattun Tsarukan Gudanar Da Tsaftataccen Zabe
- EFCC Na Binciken Ba’asin Aikin Tashar Wutar Lantarki Ta Mambila – Minista
Jam’iyyar PDP a cikin wata sabuwar kara ta bukaci da a haramtawa duk ‘yan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar a zaben 2023 da fitowa takara bayan da ake zargin an gabatar da su ne bisa sabawa kundin tsarin mulkin 1999 da dokar zaben 2022.
Karar da Mista Ayo Kamaldeen Ajibade, Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya shigar a madadin jam’iyyar PDP, ya dage kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a ranar 30 ga Satumba, 2022, wadda ta bayyana rashin bin doka da oda da ayyukan Gwamna Mai Mala Buni a matsayin Shugaban Kwamitin Taro na Musamman na Jam’iyyar APC.
Yanzu haka dai babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya sanya sabuwar kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1864/2022 ga mai shari’a Inyang Ekwo, domin yanke hukunci.
Mai shari’a Ekwo ya sanya ranar 22 ga watan Nuwamba domin gabatar da karar tare da bayar da umarnin mika dukkan mutane 53 da jam’iyyar PDP ta rubuta a cikin karar a matsayin wadanda ake kara da su bayyana a gaban kotun.