Fusatattun gwamnonin jam’iyyar PDP guda biyar (G-5) sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
An ce dan takarar na jam’iyyar APC ya nemi amincewar gwamnonin biyar din da su mara masa baya a yayin wani gangamin taro da aka gudanar a ranar Talata.
Gwamna Nyesom Wike (Rivers), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), Samuel Ortom (Benue) da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da wasu jiga-jigan siyasa daga Kudu sun sha alwashin ba za su goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ba, sabida kin amincewa da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus bayan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai sa’o’i kadan bayan ganawar da gwamnonin da Tinubu, PDP ta ce ba ta da masaniyar tattaunawar da suka yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki, inda ta ce, tasan dai kawai cewa, a halin yanzu, gwamnonin sun tafi hutu Birtaniya.
Sai dai jam’iyyar PDP ta yi barazanar hukunta gwamnonin kan duk wani aiki da zai saba wa dokokin jam’iyyar, inda ta jaddada cewa tana da karfin ladabtar da duk wani gwamna da ya bijirewa dokar Jam’iyyar.