Tsohon jigo a jam’iyyar PDP kuma mawallafin jaridar Ovation, Dele Momodu, ya kwatanta jam’iyyar da “ɗakin gawarwaki,” yana mai cewa wakilan jam’iyyar APC sun mamaye ta gaba ɗaya. Ya bayyana haka ne a cikin hirarsa da aka yi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Litinin, inda ya ce dole ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar ADC saboda PDP ta rasa tasiri da nagarta.
Momodu ya ce matakin da ya ɗauka bai saɓa da ɗabi’arsa ta siyasa ba, domin tun da farko ya saba ficewa daga jam’iyya idan ta kauce daga abin da ya dace. Ya tuna yadda a shekarar 2011 ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NCP bayan ya bar Labour Party wacce ta ƙi tsayar da ɗan takara. Duk da cewa ya samu ƙuri’u sama da dubu 26 kacal a wancan lokacin, ya ce darasin da ya koya shi ne cewa jam’iyya sabuwa ba ta da sauƙin samun nasara a Nijeriya.
- Dele Momodu Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Zuwa ADC
- Ƴan PDP Na Fice Wa Na Barin Jam’iyyar Ga Wike Da Ƴan Koransa – Dele Momodu
Ya bayyana cewa shiga PDP ya biyo bayan gamsuwa da rashin tasirin gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari. Amma a zaɓen fidda gwani na PDP a 2022, inda ya kasa samun ƙuri’a ko guda, ya fahimci cewa manyan attajirai ne ke mallakar jam’iyyar. A cewarsa, wannan ya nuna ƙarara cewa kuɗi da son zuciya sun mamaye tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyar.
Momodu ya bayyana PDP a matsayin jam’iyya mai shirin mutuwa, wacce wasu mutane ke so kawai ta ci gaba da kasancewa a ICU saboda son kai. Ya ce ba ya ganin jam’iyyar za ta iya ceto kanta daga wannan halin. Ya ƙara da cewa shi a matsayinsa na ɗan jarida da mai sharhi a harkokin jama’a zai ci gaba da lura da al’amura, amma ba zai iya zama ɓangare na jam’iyya da aka riga aka yi hijira ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp