Abubakar Abba" />

PDP Za Ta Samar Da Hanyoyin Bunkasa Rayuwar Mata –  Mariya Waziri

Shugabar  mata ta jam’iyyar PDP ta kasa Hajiya Mariya Waziri, ta bayyana aniyar jam’iyyar na bunkasa rayuwar mata ta hanyar samar musu da abubuwan ci gaban rayuwa.

Shugabar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta yi a wajen taron ranar mata ta duniya. Taken taron na bana dai shi ne, ‘samar da hanyoyin bunkasa rayuwar mata’  wanda ta ce, ya zo daidai da abin da matan Nijeriya ke bukata a siyasar kasar nan.

Shugabar ta ce jam’iyyar PDP za ta ci gaba da fafutukar ganin rayuwar mata ta inganta, a dukkan fadin kasar nan. Sannan ta ce al’umma shaida ne kan yadda jam’iyyar ta yi wa mata kokari lokacin da take kan karagar mulki.

Saboda haka, ta ci gaba da cewa, duk da haka jam’iyyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa, zaben da za a yi na shekara ta 2019, mata sun samu kashi 35 daga cikin kashi dari. Sannan kuma jam’iyyar za ta tabbatar da cewa mata sun bayar da cikakkiyar gudummawar da ya kamata su bayar wajen ci gaban tattalin arzikin kasar nan da bunkasa rayuwar al’umma.

Baya ga dukkan wadannan abubuwa, jam’iyyar ta PDP za ta ci gaba da dagewa wajen ganin mata sun samu ilimin da ya kamata da ayyukan da za su dogara da kawunansu.

Shugabar ta ci gaba da cewa, taron na su ba zai yi tuya ya manta da albasa ba, musamman a wanna rana, da suke tsanin jimamin bacewar ‘yan matan nan guda 110 na makarantar Dapchi, Saboda haka nan ma ta ce za su ci gaba da addu’a da kuma gwagwarmayar ganin wadannan ‘yan mata sun samu kubuta daga hannun ‘yan kungiyar ta Boko  Haram.

Saboda sai ta yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, karkashin mulkin jam’iyyar APC cewa, su kara zage damtse wajen ganin sun kubutar da wadannan ‘yan mata yadda za su dawo cikin iyayen da ‘yan uwansu da sauran abokan arziki su ci gaba da rayuwarsu kamar yadda kowa ke yi.

Sannan ta ci gaba da cewa, lokaci ya yi da matan jam’iyyar PDP za su hada kansu domin tunkarar zaben da za a yi a shekara ta 2019, yadda za su hada karfi wuri guda  don su samu nasara.  Ta ce samun nasarar jam’iyyar PDP a zabe ita ce samun nasararsu.

Shugabar ta ce babban burinta shi ne, mata su fahimci yadda za su samu hanyoyin ci gaban rayuwarsu, ba tunanin yadda za su yi daidai da maza ba.

Saboda haka, ta ce za su ci gaba da taimakawa matan ta kowane fannin rayuwa , ta hanyar samar musu da tsare-tsaren da za su taimaka musu wajen samun biyan bukatun rayuwarsu na yau da kullum.

Ta ce tuni shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin sun tallafawa matan kan hanyoyin da za su dogara da kansu. Saboda haka, sai ta kara da cewa yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya, domin kuwa ikon dawo da jam’yyar ta su ta karbi mulki a shekara ta 2019 na hannunsu. Saboda haka, ya zama dole a kansu su fito su zabi jam’iyyar kamar yadda ta ce.

A karshe, ta ce tana da karfin gwiwar cewa, da yardar Allah za su samu nasara a zabe mai zuwa.

Exit mobile version