Abubakar Abba" />

PENGASSAN Ta Yi Kira Da A Gaggauta Tura Dokar Mai

Kungiyar ma’aikata mai da gas ta kasa (PENGASSAN), ta yi kira ga majalisar kasa data gaggauta mayar da hankali akan sarrafa mai don cimma burin samar da sauye-sauye akan  mai da gas a kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa Kwamarade Francis Olabode Johnson ne ya bayar da wannan shawarar, inda ya yi nuni da cewar yin hakan zai inganta masana’antar ta sarrafa mai. Olabode ya yabawa ‘yan majalisar akan gabatar da dokar ta farko da skuka riga suka yi, inda ya ce ya kamata mu nuna yin ja akan bayar da kwangila da daukar ma’aikatan wucin gadi  inda hakan yake kara zamowa ruwan dare a Nijeriya.

Ya yi nuni da cewar ya kamata gwamnati ta samar da tsaro don kare rayuukan al’umma da suke gudanar da ayyukan mai da kuma kawo karshen yadda ake fasa bututun mai  domin matatun mai dake kasar nan su dinga samar da wadataccen mai da gas da ake bukata a kasar yadda masu zuba jari za su samu damar zuba jarin su da kuma samarwa da ‘yan kasa ayyukan yi.

Shugaban ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki dasu yi nazari akan kalubalen da ake fuskanta akan harkar mai da gas suke fuskanta a kasar nan don a samar da mafita. A wata sabuwar kuwa, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Ribas dasu kawo karshen haramtattun matatun mai da suke janyo karancin mai a  garin Fatakwal dake cikin jihar.

A cewar kungiyar, hayakin da haramtattun matun man suke fitarwa zai iya shafar lafiyar al’ummar dage yankin.

Shawarar wadda take kunshe a cikin sanarwar da kakakin kungiyar na kasa Mista Fortune Obi ya  fitar, ta kokan akan rashin nuna halin ko in kula akan matsalar  domin mafi yawancin mutanen da abin ya shafa suna da gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

A cewar kungiyar, hayakin yana ta faman shiga gidajen al’ummar dake yankin  haka har masu sayar da abincin sayarwa a yankin abicin su bai tsira ba.

A karshe kungiyar ta ce, ta yi hadaka da wasu kungiyoyi don wayarwa al’ummar yankin kai da kuma ankarar da gwamntin jihar akan matsalar.

 

Exit mobile version