Matatar Dangote ta yi tayin biyan ma’aikatan da ta kora cikakken albashi na tsawon shekaru biyar ba tare da sun yi aiki ba.
Matatar ta ɗauki wannan mataki ne domin hana fusatattun ma’aikatan yin ɓarna ko satar kayayyaki a matatar.
Sai dai ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN ta ƙi karɓar wannan tayin.
Maimakon haka, ta dage cewa a sake dawo da ma’aikatan bakin aikinsu ko kuma tura su zuwa wasu sassa na kamfanonin Dangote ba tare da rage musu albashi ba.
Bayan shiga tsakani daga gwamnati ta yi, an cimma yarjejeniya cewa za a dawo sa ma’aikatan da aka sallama zuwa wasu rassa na kamfanin Dangote, za a kare musu albashinsu, kuma ba za a hukunta kowa kan rikicin da suka haddasa ba.
Wannan al’amari ya nuna yadda ake samun ƙarin rashin jituwa tsakanin shugabancin kamfanin da ƙungiyoyin ƙwadago, duk da cewa matatar ana ganin ta zama muhimmin ginshiƙi wajen cikar burin Nijeriya na cin gashin kai a fannin makamashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp