Kwanan nan, babban jirgin ruwan ‘yan sandan kasar Philippines mai lamba 9701 ya yi aiki a tekun kusa da tsibirin Huangyan na kasar Sin, inda sau da yawa ya bi bayan jiragen ruwan ‘yan sandan teku na kasar Sin mai lamba 21550 da 5009, har ma kusancinsu bai wuce mita dari ba, inda hakan ya haifar da babbar barazana ga tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa na ‘yan sandan teku na kasar Sin.
Ba kamar yadda ya saba da nuna siffar “marasa karfi” a baya ba, a wannan karo, jirgin ruwan ‘yan sandan teku na kasar ya dauki mataki mai hadari na kusantar jiragen ruwan kasar Sin, wanda ya nuna ra’ayinsa na tada fitina, da mummunar kasadar manufofin gwamnatin Philippines kan batun tekun kudancin kasar Sin.
Bana ta cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin ’yan mulkin danniya na duniya. Ya kamata a koyi darasi daga tarihi ta yadda za a iya fuskantar nan gaba. Yanzu mutane suna kara kishin zaman lafiya, kuma ana ta karfafa niyyar mayar da tekun kudancin kasar Sin da ya zama teku mai zaman lafiya.
Kasar Philippines ta manta da darussan da aka koya daga tarihi, kuma ta koma baya a yayin da ake samun ci gaban zamani, har ma ta kasance tushen haddasa tashe-tsashen hankula a tekun kudancin kasar Sin. Shin har yanzu gwamnatin Philippines ba ta gane ba? Ko shakka babu za ta zama ganima a yayin da aka farauci mai farautowa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp