Abba Ibrahim Wada" />

Pogba Ya Raina Mourinho, In Ji Paul Scholes

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Scholes, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, wanda yafi kowa tsada, Paul Scholes ya raina Mourinho sakamakon irin kwallon daya buga a wasan kungiyar da Westbrom.

Scholes ya bayyana hakane a hirarsa da wani gidan talabijin inda yace irin yadda ya buga kwallo a wasan da suka sha kashi har gida a hannun Westbrom ya rainawa Mourinho hankali saboda wasansa kawai ya buga  a wasan.

Yaci gaba da cewa bai buga wani abun kirki ba a wasan kawai tsalle-tsallensa yayi acikin filin saboda haka Mourinho yayi dai-dai daya cireshi a minti na 58 da fara wasan domin ya gane cewa baya kokari yadda yakamata.

Ya kara da cewa ba kawai Pogba bane baya kokari, shima dan wasan da kungiyar ta siyo kuma yafi kowanne dan wasa daukar albashi, Aledis Sanches, baya kokari kuma yakamata yafara nunawa duniya cewa shine Sanches din da aka gani a Barcelona ta Arsenal.

A karshe yace Pogba da Sanches babu kamarsu a kungiyar saboda haka yakamata su fara nunawa duniya cewa zasu iya rike ragamar Manchester United nan da wasu yan shekaru idan kuma ba haka ba tabbas siyansu bashi da amfani.

Manchester United dai itace a matsayi na biyu akan teburin firimiya sannan kuma zata buga wasan kusa dana karshe da kungiyar Tottenham a ranar Asabar a gasar cin kofin kalubale na FA.

Exit mobile version