Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Pompeo Na Son Sarrafa Kungiyar EU Kamar Wata ‘Yar Amshin-shata

Published

on

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, wani mutum ne da ya kware a fannin haddasa tunzuri tsakanin mutane. Sa’an nan a kwanan nan, ya fara mai da hankali kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, inda ta yi ta kokarin lallashin kasashen Turan, domin su yi hadin gwiwa da kasar Amurka, a kokarinta na jayayya da kasar Sin.
Ana iya cewa, yana neman yin amfani da kungiyar tarayyar Turai ta EU ne, a matsayin wata ‘yar amshin-shata a hannunsa, don neman samar da wani yanayi na nuna kiyaya ga kasar Sin a duniya.
Sai dai ko da yake mista Pompeo ya yi kokarin samar da tasiri kan kungiyar EU, amma shugabannin kungiyar ba za su yarda su zama ‘yan barandan kasar Amurka ba. A ko da yaushe, kungiyar EU tana nuna sanin ya kamata, da dogaro da kai, yayin da take tsara manufofinta masu alaka da kasar Sin.
Dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, kasancewar ana samu moriyar bai daya da dimbin bukatun hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. Sa’an nan a matsayinsu na wasu muhimman bangarori guda 2 a duniya, kasar Sin da kungiyar EU, suna da matsaya daya dangane da wasu manyan batutuwa masu muhimmanci da yawa, lamarin da ya sa suka fi yin hadin kai da juna maimakon gogayya da juna.
Kasashen Turai sun fahimci cewa, ko a fannin dakile cutar COVID-19, ko kuma a fannin farfado da tattalin arzikin duniya, ba za a iya kauracewa hadin gwiwa da kasar Sin ba. Kuma yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2 ya dace da yanayin zamanin da muke ciki, hakan ne kuma dalilin da ya hana mista Pompeo samun damar lalata huldar dake tsakanin Sin da Turai.
Tun daga ranar 1 ga watan Yuli, kungiyar EU ta bude kan iyakokinta ga wasu kasashe, amma ban da kasar Amurka, ta la’akari da matsanancin yanayin da kasar Amurka ke ciki a fannin dakile cutar COVID-19. Hakan ya nuna yadda kasashen Turai suka ki amincewa da aikin hana yaduwar annoba da ake yi a kasar Amurka. Kuma ko shakka babu, ‘Yan siyasar kasar Amurka irin Mike Pompeo, ba za su ji dadin hakan ba. (Bello Wang)
Advertisement

labarai